Yankari: Dalibai hudu sun mutu, an kwantar da 12 a asibiti bayan dawo wa daga wurin shakata wa a Bauchi

Yankari: Dalibai hudu sun mutu, an kwantar da 12 a asibiti bayan dawo wa daga wurin shakata wa a Bauchi

Wani lamari mai ban tausayi, tayar da hankali da cike da fargaba ya faru ga daliban wata kwalejin ilimi dake Waka-Biu a karamar hukumar Biu dake jihar Borno, bayan daliban makarantar hudu sun mutu, an kwantar wasu 12 a asibiti bayan dawowar su daga yawon bude a wurin shakatawar nan dake Yankari a jihar Bauchi.

An tabbar da mutuwar a kalla mutane hudu daga cikin daliban yayin da aka kwantar da wasu 12 a asibiti, inda ake duba lafiyarsu.

Wasu bayanai sun nuna cewa daliban sun fara nuna alamomin rashin lafiya tun bayan dawowarsu da wurin shakatarwar dake jihar Bauchi.

An bayyana cewa daliban suka mutu sun dinga yin aman jini kuma sun mutu cikin kankanin lokaci kafin a gano menene ke damunsu.

Daga cikin daliban da suka mutu akwai diyar shugaban karamar hukumar Biu, wacce ita na daga cikin wadanda suka je ziyarar.

Jaridar Premium Times ta ce shugaban makarantar ya sanar da su cewa wannan ba shine karo na farko da daliban suka taba kai ziyara dajin Yankari ba.

"Daliban mu kan ziyarci wannan wuri duk shekara domin yana daga cikin darussan da ake koya musu. Muna raba daliban zuwa rukuni-rukuni domin yin tafiyar cikin sauki, rukuni na farko da na biyu sun je sun dawo lafiya. Wadannan sune rukuni na uku da suka yi tafiyar, kuma bayan dawowarsu ne aka fara samun bayanan cewa wasu basu da lafiya.

DUBA WANNAN: Hare-haren daukan fansa: DSTV da MTN sun rufe ofisoshinsu na Kano

"Yanzu haka an killace duk daliban da suka yi tafiyar domin gudanar da bincike a kan lafiyarsu. An kwantar da wasu 12 daga cikinsu biyo bayan alamun tsananin rashin lafiya da suka nuna, ana duba lafiyarsu a babban asibiti a Maiduguri.

Har yanzu ba gano a wurin da daliban suka kamu da wannan cuta ba, kuma ba a san wacce irin cuta ba ce.

Sai dai, wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu dalibai da suka ziyarci Yankari daga jihar Kano sun taba fuskantar irin wannan matsala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel