Kafin karshen watan Satumba zamu fitar da kasafin kudin 2020 – Zainab Ahmed

Kafin karshen watan Satumba zamu fitar da kasafin kudin 2020 – Zainab Ahmed

Ministar kudi, tsare-tsare da kuma kasafin kudin kasa, Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya na cigaba da yin kokarin ganin cewa ta mikawa majalisar dokoki kasafin kudin shekara mai zuwa kafin karshen watan Satumba.

Da take magana a wurin wani taron na musamman da ya shafi tattaunawa a kan kasafin kudin shekarar 2020 ranar Laraba a Abuja, ministar ta ce tuni aka soma shirin fitar da kasafin kudin 2020.

KU KARANTA:Yabon gwani ya zama dole: An jinjinawa wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello bayan da ya mayar da wayar tsintuwa ga mai ita

Bugu da kari, ta fadi wasu abubuwa guda 11 na bangaren tattalin arziki wadanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta mayar da hankali a kansu.

A cewar ministar daga cikin wadannan abubuwa 11 akwai samar da tattalin arziki mai karfi wanda zai taimakawa masu kananan sana’o’i, yaki da cin hanci da kuma samar da kudaden tallafi ta hanyar shirye-shirye gwamnati na musamman.

Har ila yau, akwai bukatar zuba hannun jari a bangaren ayyukan raya kasa, bunkasa jama’a ta yadda za’a sama masu aikin yi da kuma bangaren kula da lafiya, a cewarta.

“Muna da shirin samar da walwala ga al’umma Najeriya a bangarori daban-daban, tsaro, harkar noma, gidaje musamman ga ma’aikata da sauransu su ne kan gaba a cikin ayyukan da wannan kasafin kudin na shekarar 2020 zai fi mayar da hankali a kansu.” Inji Zainab Ahmed.

A wani labarin mai kama da wannan, za ku ji cewa Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya ce majalisarsu ba zata bata lokaci wajen bitar kasafin kudin shekara mai zuwa ba.

A cewar kakakin da zarar Shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudin za su dukufa domin yin aiki a kansa wanda za su kammala kafin shekarar nan ta kare.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel