Da dumi dumi: Kotu ta fatattaki jigon jam’iyyar APC daga majalisar wakilai

Da dumi dumi: Kotu ta fatattaki jigon jam’iyyar APC daga majalisar wakilai

Wani dan majalisar wakilai daga jahar Cross Rivers, kuma kusa a jam’iyyar APC, Alex Egbona ya rasa kujerarsa sakamakon wani hukunci da kotun sauraron korafe korafe ta yanke a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba a garin Calabar.

Jaridar Punch ta ruwaito tsohon kaakakin majalisar dokokin jahar Cross Rivers, kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019, John Gaul-Leo ne ya shigar da karar Alex inda ya kalubalanci nasarar daya samu a zaben ranar 23 ga watan Feburairu na 2019.

KU KARANTA: Ba zan sadaukar da wata makaranta don gina kwalejin kimiyya a Daura ba – Masari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kotun bayyana Alex a matsayin haramtaccen wakilin mazabar Abi/Yakurr a na jahar Cross Rivers a majalisar wakilan Najeriya, inda ta bayyana cewa tun farko ba Alex bane halastaccen dan takarar jam’aiyyar APC.

Da yake yanke hukunci, shugaban Alkalan kotun, mai sharia Vincent Agabata ya bayyana cewa Alex na jam’iyayr APC bai cancanci tsayawa takara ba balle har ya fafata a zaben dan majalisa, don haka dukkanin kuri’un daya samu basu halasta ba

Da wannan ne Alkalin ya yanke hukuncin cewa “John Gaul Leo dan takarar jam’iyyar PDP, shi ne halastaccen dan majalisa mai wakiltar mazabar Abi-Yakurr a majalisar wakilai bayan ya samu halastattun kuri’un da suka fi yawa a zaben 2019, don haka hukumar INEC ta janye shaidar samun nasara data baiwa Alex ta baiwa John Gaul-Leo.”

A wani labarin kuma, wata kotun sauraron korafe korafen zaben yan majalisu dake zamanta a jahar Benuwe ta soke nasarar dan majalisa mai wakiltar mazabar gboko ta yamma a majalisar wakilai, Terna Achii ya samu a karkashin jam’iyyar PDP.

Shugaban Alkalan kotun sauraron korafe korafen, mai sharia A.A Adeyeye yayin da yake hukunci ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar PDP, Terna Achii bai ci zaben da mafi yawan kuri’u ba, don haka nasarar daya samu a baya ta haramta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel