Babban dan sanda daya ya mutu, uku sun samu rauni bayan kama yaran Wadume

Babban dan sanda daya ya mutu, uku sun samu rauni bayan kama yaran Wadume

Wani babban dan sanda daya mai mukamin 'Insifekta' ya mutu a daren ranar Litinin yayin da wasu hudu suka samu raunuka bayan motar jami'an tsaron 'yan sanda na rundunar IRT (Intelligence Response Team) ta yi hatsari a kan hanyar Wukari a Ibi dake jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne yayin da jami'an 'yan sanda ke tafiya a motarsu kirar 'Toyota Hiace' a hanyarsu ta dawo wa daga kamen wasu da ake zargin suna da alaka ta kusa da babban mai garkuwa da mutanen nan da aka kama, wato Alhaji Hassan Bala (da aka fi kira Wadume).

Tawagar 'yan sandan mai jami'ai guda takwas a karkashin jagorancin ASP James Bawa ta gamu da tsautsayin ne a kan hayarsu ta zuwa Wukari bayan sun kama masu laifin da ake zargin na da alaka da Wadume

Rahotanni sun bayyana cewa motar da jami'an tsaron da masu laifin ke ciki ta yi hatsari ne sakamakon fashewar daya daga cikin tayoyin ta, lamarin da yasa motar ta kayar da su.

DUBA WANNAN: DSTV da MTN sun rufe ofisoshinsu na Kano

Jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa wani jami'in dan sanda da aka bayyana sunasa da Clement ya mutu nan take, yayin da ragowar jami'an 'yan sanda da masu laifin suka samu raunuka.

Kazalika, jaridar ta ce an kawo wa mutanen cikin motar agaji kuma an garzaya da su zuwa asibiti mafi kusa.

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya tabbatar da faruwar hatsarin ga jaridar, amma ya ce bai samu isassun bayanai a kan abinda ya faru ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel