Yabon gwani ya zama dole: An jinjinawa wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello bayan da ya mayar da wayar tsintuwa ga mai ita

Yabon gwani ya zama dole: An jinjinawa wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello bayan da ya mayar da wayar tsintuwa ga mai ita

Wani dalibin Ilimin zamantakewa na Jami’ar Ahmadu Bello dake karatunsa a Kwalejin Ilimi ta Zaria wato FCE Zaria, ya samu yabo a ranar Laraba bayan da ya mayar da wata wayar salula da ya tsinta zuwa hannun mai ita.

Majiyar Daily Trust ta ruwaito cewa dalibin mai suna, Isma’il Salisu Rogo wanda ya fito daga jihar Kano ya yi arba da wayar ne kirar Infinix wadda aka kiyasta kudinta zai kai N120,000 a bisa tebur yayin da ya shiga wani aji domin yin karatu.

KU KARANTA:Ruga: Matawalle ya ware biliyan N8.631 domin aiwatar da aikin a jihar Zamfara

Ya kara da cewa: “A bisa tebur na ga wayar a shimfide. Na matsa kusa na dauki wayar kana na garzaya wurin daya daga cikin malamanmu domin kai masa rahoto. Muna tsaye tare da shin a kira mai wayar cewa ta zo ta karbi wayarta.

“Na sha surutai iri-iri a dalilin mayar da wannan waya da nayi. Ko kadan ni ban damu da abinda wasu daga cikin abokan nawa ke fadi ba saboda nasan barawo dai sunansa barawo walau miliyoyi ya sata ko kuma wayar salula.” A cewar Salisu.

Dakta Abdulhadi Gambo wanda yake malami kuma tsohon shugaban sashen ilimin zamantakewa dake a kwalejin FCE Zaria ya na daya daga cikin wadanda suka jinjinawa irin wannan namijin aiki.

A cewar Abdulhadi: “Da dama daga cikin dalibai na fuskantar matsananciyar wahala kafin samun abinci. A don haka ya zama wajibi ga mai nema ya kasance na kirki domin ya rika ganin cigaba da budi a rayuwarsa. Ina fatan sauran dalibai za suyi koyi da irin wannan hali na gari.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel