Da yawan 'yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu safarar miyagun kwayoyi suke - Minista

Da yawan 'yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu safarar miyagun kwayoyi suke - Minista

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ministar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu, Naledi Pandor, ta zargi da yawa daga cikin 'yan Najeriya mazauna kasar da aikata laifuka na fataucin muggan kwayoyi da sauran miyagun laifuka.

"Duk da cewa ina alfahari 'yan Najeriya na bayar da gudunmuwa mai tarin yawa wajen tabbatar da akidar al'ummar kasar mu da kuma bunkasa ci gaba, sai dai babu shakka da yawan su sun kasance suna aikata miyagun laifuka na safarar muggan kwayoyi."

"Tabbatar da cewa ire-iren wannan miyagun mutane ba su shigo kasar mu ba, zai taimaka kwarai da aniya wajen wanzar da aminci a kasar" inji Pandor kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Pandor a yayin wata hirarta da 'eNCA', wata kafar watsa labarai a yanar gizo da ke kasar Afirka ta Kudu, ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kawo masu dauki na tsarkake kasar daga fataucin miyagun kwayoyi domin tabbatar da aminci.

Pandor ta ce babu shakka gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta na sane da mummunar akidar kin jinin baki da ta dabaibaye kasar, lamarin da ta ce gwamnatin su ta daura damarar magance wannan barazana cikin gaggawa.

Ana iya tuna cewa a ranar Larabar ta gabata ne shugaban kasa Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, suka shiga bayan labule dangane da tababar kin jinin baki da ake yi a kasar Afirka Ta Kudu, biyo bayan hare-haren da aka zartar kan 'yan Najeriya a kwana-kwanan nan.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta aike wa jakadan Afirka Ta Kudu a kasar, Mista Bobby Moroe sammaci kan hare-haren kin jinin baki da ake kai wa 'yan Najeriya a kasar da yake wakilta.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ba za ta sake bari a taba kudin kananan hukumomi ba - Boss Mustapha

Haka zalika, ministan harkokin kasashen ketare, Mr Onyeama, ya gana da jakadan Afirka Ta Kudu a ranar Talatar da ta gabata kan kashe-kashe na baya-bayan nan da aka fara a karshen makon nan.

A cewar ministan, daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka akwai batun hadin gwiwa a tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu, lamarin da Ministan ya ce zai bai wa jami'an tsaron Najeriya da ke ofishin jakadanci Najeriya a kasar Afrika ta Kudu damar aiki tare da takwarorinsu na kasar domin bayar da kariya ga 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta kuma bukaci gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta fara biyan diyya ga dukkan 'yan Najeriya da hare-haren ya shafa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel