Gwamnatin Tarayya ba za ta sake bari a taba kudin kananan hukumomi ba - Boss Mustapha

Gwamnatin Tarayya ba za ta sake bari a taba kudin kananan hukumomi ba - Boss Mustapha

A wani rahoto da muka kalato daga jaridar The Cable, babban sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta sake bari a taba kudaden kananan hukumomi.

Sakataren gwamnatin ya jadadda kudirin gwamnatin tarayyar Najeriya na raba asusun hadin gwiwa na gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi.

Furucin Boss Mustapha na kunshe ne a cikin wata sanarwa yayin taron kula da kananan hukumomi da aka gudanar a babban birnin kasar nan na tarayya.

David Attah, babban daraktan kula da ayyuka na musamman wanda ya wakilci sakataren gwamnatin a yayin taron, ya zargi gwamnatocin jihohi da ta tatse asusun kudi da aka tanada domin kananan hukumomi.

Ya ke cewa, akwai bukatar kananan hukumomi su samu cin gashin kai da kuma 'yancin gudanar da al'amuran kudi da aka tanadar masu, lamarin da ya ce hakan zai ba su damar biyan bukatun al'ummomin su tun daga tushe.

KARANTA KUMA: Dalibai 4 sun mutu, 12 na jinya yayin da bakuwar cuta ta bulla a wata kwalejin Borno

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, al'ummar Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana gwamnatocin jihohi taba kudaden kananan hukumomi a tsarin da suke bi na asusun hadin-gwiwa.

Hukumar da ke tattara bayanan sirri a kan laifukan da suka shafi kudi da ta`addanci ta kasar NFIU ce ta sanar da cewa, daga watan Yunin da ya gabata ne za a haramtawa gwamnatocin jihohi amfani da kudaden kananan hukumomi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel