Dalibai 4 sun mutu, 12 na jinya yayin da bakuwar cuta ta bulla a wata kwalejin Borno

Dalibai 4 sun mutu, 12 na jinya yayin da bakuwar cuta ta bulla a wata kwalejin Borno

Yanayi na dimuwa gami da faduwar gaba ya afka wa daliban wata Kwalejin Ilimi da ke Waka-Biu a karamar hukumar Biu ta jihar Borno, yayin da wasu daliban makarantar suka rika mutuwa a bayan dawowarsu daga yawon bude ido.

Rahotanni sun bayyana cewa, jim kadan bayan dawowa daga yawon bude a wurin shakatawa na Yankari da ke jihar Bauchi, wata bakuwar cuta ta ciwon ciki da aman jini, ta kar dalibai hudu yayin da 12 ke jinya kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Da ya ke ganawa da manema labarai yayin tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari, shugaban kwalejin Muhammad Audu, ya musanta jita-jitar da ke yaduwa kan cewa adadin rayuka 9 ne suka salwanta.

Audu ya ce wannan ba shi ne karo na farko da daliban kwalejin suka ziyarci wurin shakatarwa ba, yayin da suka saba ziyarta a kowace shekara domin bude ido kasancewarsa wani bigire cikin nazarin karatun su.

KARANTA KUMA: Watan Agusta: Rayuka 53 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 73 a fadin Najeriya

Kazalika mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Kadafur, yayin bayar da tabbacin sa a kan aukuwar wannan annoba, ya ce daya daga cikin daliban da suka riga mu gidan gaskiya, Adama Dika, ta kasance diya ga mukaddashin shugaban karamar hukumar Biu, Usman Dika.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel