Watan Agusta: Rayuka 53 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 73 a fadin Najeriya

Watan Agusta: Rayuka 53 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 73 a fadin Najeriya

Babu shakka rayukan al'umma musamman a Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar barazana a sanadiyar munanan hare-hare na ta'addancin masu garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma, hare-haren 'yan daban daji da kuma kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

A wani rahoto da jaridar Premium Times ta ruwaito, akalla rayukan mutane 53 sun salwanta a sanadiyar aukuwar munanan hare-hare, yayin da mutane 73 suka afka tarkon masu garkuwa a fadin Najeriya cikin watan Agustan da ya gabata.

Sai dai cikin wannan sabuwar kididdiga da aka fitar, an samu rangwami na adadin rayukan da suk salwanta a sanadiyar aukuwar hare-hare cikin watan Agusta idan an kwatanta da watannin da suka shude a baya.

Rahotanni daga kafofin watsa labarai da kuma hukumar 'yan sanda sun bayyana cewa, rayukan mutane 353 ne suka salwanta a sanadiyar munanan hare-haren da suka auku a watan Yuni. Haka zalika mutane 60 ne sun afka tarkon masu garkuwa da mutane a watan.

A watan Yuli kuma, mutane 97 ne suka shiga tarkon masu garkuwa da neman kudin fansa, yayin da rayuka 282 suka salwanta a sanadiyar munanan hare-haren da suka auku a fadin Najeriya.

A watan jiya dai da ya kasance watan Yuni, jihar Katsina wadda ta kasance mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta jagoranci sauran jihohin Najeriya ta fuskar girman asara da ta'addanci ya janyo mata.

Dalla Dalla ga dai yadda lamari na ta'addanci ya kasance cikin wasu da dama daga jihohin kasar nan a watan na Agusta kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa:

Katsina: Rayuka - 4 Garkuwa - 50

Benuwe: Rayuka - 9 Garkuwa - 0

Taraba: Rayuka - 8 Garkuwa - 0

Kaduna: Rayuka - 6 Garkuwa - 12

Ogun: Rayuka - 5 Garkuwa - 0

Nasarawa: Rayuka - 4 Garkuwa - 0

Borno: Rayuka - 3 Garkuwa - 0

Rivers: Rayuka - 3 Garkuwa - 0

Kogi: Rayuka - 3 Garkuwa - 0

Legas: Rayuka - 3 Garkuwa - 0

Enugu: Rayuka - 2 Garkuwa - 0

Ondo: Rayuka - 2 Garkuwa - 0

KARANTA KUMA: Kin jinin baki a Afirka ta Kudu: Matakin da Buhari ya dauka ba su wadatar ba - Sule Lamido

Edo: Rayuka - 2 Garkuwa - 1

Anambra: Rayuka - 1 Garkuwa - 0

Abia: Rayuka - 1 Garkuwa - 0

Adamawa: Rayuka - 0 Garkuwa - 1

Sakkwato: Rayuka - 0 Garkuwa - 1

Imo: Rayuka - 0 Garkuwa - 1

Abuja: Rayuka - 0 Garkuwa - 1

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel