Kin jinin baki a Afirka ta Kudu: Matakin da Buhari ya dauka ba su wadatar ba - Sule Lamido

Kin jinin baki a Afirka ta Kudu: Matakin da Buhari ya dauka ba su wadatar ba - Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka kan ci gaba da kai farmaki da munanan hare-hare na kin jinin al'ummar Najeriya a kasar Afirka ta Kudu ba su wadata ba.

Alhaji Lamido yayin ganawa da manema labarai na jaridar Premium Times a ranar ALhamis, ya shawarci shugaba Buhari da ya zayyana wa alummar kasar nan matakan da ya dauka wajen kawo karshen wannan mummunan lamari na cin kashi da ake yi wa 'yan uwansu mazauna kasar Afirka ta Kudu.

A cikin shawarwari da tsohon gwamnan ya gabatar, ya nemi shugaba Buhari da ya fito ya yi magana da fatun bakinsa, domin kuwa a cewar gwamnan wannan babban lamari ne da ya sha gaban duk wata sanarwa da za ta fito daga bakin hadiman sa kadai.

Haka zalika tsohon gwamnan ya nemi hadiman shugaba Buhari da su shawarci ubangidansu a kan lallai ya fito ya yi magana a karan kansa dangane da wannan lamari domin kara wa al'ummar Najeriya kwarin gwiwa da kuma sanya aminci a zukatansu.

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, hadiman shugaban kasa a kan kafofin sada zumunta na zamani, Lauretta Onochie, ta wallafa wasu matakai takwas da gwamnatin tarayya ta dauka dangane da tababar kin jinin baki a Afirka ta Kudu.

Cikin jerin matakan da Mrs Onochie ta wallafa a shafin ta na Twitter a ranar Larabar da ta gabata sun hadar da:

1. Gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta fara biyan diyya ga dukkanin 'yan Najeriya da hare-haren ya shafa.

2. Gwamnatin Najeriya ta nemi a tabbatar da adalci ta hanyar hukunta wadanda ke da hannu wajen zartar da wannan munanan hare-hare.

3. Shugaba Buhari ya aika da jakada na musamman zuwa kasar Afirka ta Kudu domin bayyana rashin dadinsa kan wannan cin zarafi.

4. Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai dangane da rashin kulawa ta hukumomin tsaron kasar Afirka ta Kudu, a yayin da suka gaza bai wa 'yan Najeriya kariya da kuma tsare rayuka da dukiyoyinsu.

5. Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce mun ja layi kuma hakurin Najeriya ya kare kan irin hare haren da 'yan Afirka ta Kudu ke kaiwa kan yan kasar ta mazauna can.

KARANTA KUMA: APC ta ci gaba da rike hukuncin dakatar da Abdulmumin Kofa

6. Najeriya ta janye jakadanta da ke Afirika ta Kudu, Kabir Bala yayin da ta kuma fice daga taron tattalin arzikin duniya da aka fara gudanarwa a birnin Cape Town a Laraba saboda hare-haren da ake kai wa ‘yan kasarta.

7. Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kausasa harshe tare da bayyana bacin rai akan wannan lamari, inda ya ce mahukuntan Afirka ta Kudu su fito su yi bayani da babban baki.

8. Gwamnatin Najeriya a yanzu tana kalubalantar kasar Afirka ta Kudu da ta kawo karshen wannan kin jini da kyamar baki cikin gaggawa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel