Yanzu-yanzu: Zaluntana aka yi, ba zan yarda ba - Dino Melaye

Yanzu-yanzu: Zaluntana aka yi, ba zan yarda ba - Dino Melaye

Sanata mai wakilatan Kogi ta yamma kuma dan takaran gwamnan jihar Kogi, Dino Melaye, ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon zaben fidda gwanin PDP a takarar gwamnan jihar Kogi.

Sanatan ya nuna bacin ransa inda ya bayyana cewa akwatuna biyu cikin takwas kadai aka kirga kuri'unsa.

Ya ce ta yaya za'a alanta wanda ya lashe zabe bayan an nemi kuri'unsa dake cikin akwatuna takwas an rasa.

Yace: "Abin takaici ne a alanta sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Kogi yayinda aka nemi kuri'una dake cikin akwatuna takwas aka rasa. Kawai sai a kirga kuri'una na cikin akwatuna biyu kadai. Ba zan yarda da hakan ba."

KU KARANTA: Matar aure ta gurfanar da malaminta gaban kotun Kano saboda yana nemanta da zina

Mun kawo muku rahoton cewa Injiniya Musa Wada ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar Kogi na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da aka gudanar yau Laraba, 4 ga watan Satumba, 2019.

Musa Wada, wanda yake kani ga tsohon gwamnan jihar Kogi kuma yayi takara a zaben, Idris Wada, ya lallasa sauran yan takaran inda ya samu kuri'u 748.

Dan tsohon gwamnan jihar Ibrahim Idris, Abubakar Ibrahim, ne ya zo na biyu d kuri'u 710, sai Idris Wada wanda ya zo na uku.

Ga sakamakon zaben: Musa Wada - 748 Abubakar Mohammed Ibrahim - 710 Capt. Idris Wada - 345 Dino Melaye - 70 Aminu Suleiman- 55 Victor Adoji-54, Erico Joseph- 42, AVM Saliu Atawodi (retd.)- 11, Emmanuel Omebije- 9 Mohammed Shuaibi- 4 Bayo Michael- 2 Jabiru Haruna- 0.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel