Ku fallasa karuwai a duk wani lungu da sako – Hukumar Hisbah ga jama’ar Kano

Ku fallasa karuwai a duk wani lungu da sako – Hukumar Hisbah ga jama’ar Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi kira ga al’umma da su kai rahoto sannan su fallasa ayyukan karuwai a yankunansu domin samun ci gaba a jihar cikin sauri.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga kakakin hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim sannan ya isar dashi ga manema labarai a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba a Kano.

Kwamanda Janar na hukumar, Sheikh Harun Ibn-Sina ya yi wannan roko yayinda yake jawabi ga wata wadanda jami’an Hisbah kama suna yawo a wasu unguwannin birnin da tsakar dare.

Ibn-Sina ya bayyana cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar dukkanin laifuffuka a garin musamman ma karuwanci.

Yace: “Mafi akasarin wadanda jami’an Hisbah suka kama a lokacin sintirin sun kasance yara mata.

“An kai mamayar ne a hanyar Church Road da ke Sabon Gari, Railway quaters, hanyar Tukur da ke Nasarawa GRA da kuma hanyar Sarkin Yaki a Kano.”

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Yan gida daya mutum 7 sun mutu a lokaci guda

Ya ci gaba da bayanin cewa za a hukunta wadanda aka kama da hakan daidai da doka domin ya zamo izina ga sauran mutane.

Kwamanda Janar din yace za a yi wa matan da aka kama jawabi da jan hankali kafin a mika su ga iyayensu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel