Ruga: Matawalle ya ware biliyan N8.631 domin aiwatar da aikin a jihar Zamfara

Ruga: Matawalle ya ware biliyan N8.631 domin aiwatar da aikin a jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a ranar Laraba ya kaddamar da aikin killace wurin kiwo ga makiyaya a kan zunzurutun kudi naira biliyan 8.631 a jejin Rinji Sakkida dake a karamar hukumar Maradun.

Da yake magana a lokacin kaddamar da wannan shirin Matawalle ya ce manufar aiwatar da wannan shirin shi ne domin a inganta rayuwar Fulani makiyaya ta yadda tsarin kiwonsu zai rika tafiya daidai da zamani.

KU KARANTA:David Lyon ya lashe zaben fidda gwani na APC a Bayelsa

“A cikin ‘yan shekarun da suka shude babbar matsalar dake addabar yankin nan namu ita ce rikici tsakanin manoma da makiyaya. Babu kuwa abinda ke kawo fadan idan ba karancin wuraren da dabbobin za su domin samun abinci ba.

“Kamar yadda muka sani a cikin ‘yan kwanakin nan, rikicin ya dauki wani sabon salo. Salon da ba mu taba ganin irinsa ba. A irin cigaba da aka samu yanzu a kasashen duniya an bar yin kiwon dabbobi irin na yawo ko kuma kara zube.

“Abinda ake yi kuwa shi ne killace dabbobin tare da sama masu abinci da ruwan sha a wurin da suke zaune ba tare da an yawata da su ba. A dalilin wannan shirin Ruga zai taimaka matuka wurin kawo zaman lafiya a jiharmu musamman a tsakanin manoma da makiyaya.” Inji Matawalle.

Majiyar jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnan ya kara da cewa zaman lafiya shi ne ginshiki da ko wace gwamnati ke amfani da shi domin aiwatar da ayyukan na cigaba ga al’ummarta. Ya kuma sake cewa za ayi ginin rugar ne a yankunan jihar guda uku inda ko wace za ta samu guda daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel