DSTV da MTN sun rufe ofisoshinsu na Kano

DSTV da MTN sun rufe ofisoshinsu na Kano

A yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da kai harin daukan fansa a kan masana'antu da kamfanoni mallakin kasar Afrika ta Kudu a sassan Najeriya, musamman a yankin kudu, DSTV da MTN sun rufe ofisoshinsu da ke Kano na wucin gadi.

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewa an rufe ofishin MTN na Kano dake Nasarawa GRA bisa umarnin da aka aiko wa ofishin daga sama, saboda akwai isassun jami'an tsaro dake gadin ofishin tun bayan fara kai hare-haren daukar fansa a ranar Talata.

Jaridar Solacebase.com ta ce wakilinta ya ga jami'an tsaro sun kwace wayar wani matashi da ya yi kokarin daukan hoton ofishin a ranar Laraba.

Kazalika, jaridar ta ce wakilinta da ya ziyarci ofishin kamfanin DSTV, ya ga motoci biyu na jami'an 'yan sanda da wata mota guda ta jami'an hukumar NSCDC da aka fi kira da 'civil defence'.

Jaridar ta ce hatta a cikin sakon da kamfanin MTN ya aike mata, ya sanar da cewa sun rufe shagunan a yau (Laraba) tare da bayyana cewa za a iya samun su a kan manhajar Tuwita a kan sunan 'MTN180'

DUBA WANNAN: Babbar magana: Kotu ta bayar da umarnin kwace kadarorin tsohon gwamnan APC da matarsa

An bayyana cewa harkoki sun ja baya a katafaren sayar da kaya na 'Shoprite' tare da ganin bakin jami'an tsaro suna muzurai a haraba da cikin shagon.

Majiyar mu ta sanar da mu cewa harkokin sun wakana a bankin IBTC dake kan titin Bank 'Road' kamar kullum, ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.

Wutar kai hare-haren daukan fansa a kan masana'antu da kamfanoni mallakar Afrika ta Kudu ta ruru cikin kankanin lokaci, kuma ana tsoron cewa zata iya fantsama zuwa yankin arewacin Najeriya, musamman a manyan birane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel