Tsaffin ma'aikatan gwamnatin jihar Benue masu murabus sun tayar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar

Tsaffin ma'aikatan gwamnatin jihar Benue masu murabus sun tayar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar

- Tsoffin ma'aikatan jihar Benue masu murabus sun tada zanga-zanga a kan hakkokinsu

- Ma'aikatan sun zagaye gidan gwamnatin jihar ne da alkawarin ba za su bar wajen ba sai an biyasu kudadensu da aka rike na watanni 25

- Ma'aikatan sun koka da halin ko-in-kula da gwamnatin ta nuna mu su wanda hakan yasa suke rasa 'yan kungiyar fanshon

A jiya Laraba, tsoffin ma'aikata da su ka yi murabus, sun mamaye gidan gwamnatin jihar da ke Makurdi inda har suka hana ababen hawa wucewa.

A makon da ya gabata ne tsoffin ma'aikatan su ka yi alkawarin yin zanga-zanga matukar ba a biyasu hakkokinsu da ya hada da kudin fansho da na sallamar aiki ba da ya kai naira biliyan 28.

Masu zanga-zangar sun dau takardu masu rubuce-rubuce irin su, 'Ortom, biyamu hakkokinmu da ka rike na tsawon watanni 25, ya isa haka,' 'Gwamna Ortom baya jihar Benue, satin sa uku a Amurka da Japan, a kan me?' da dai sauran ire-iren rubutu masu nuna fusatar ma'aikatan.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Shugaban 'yan fanshon, Peter Kyado, wanda ya jagoranci zanga-zangar, ya zargi cewa kungiyar na rasa mutane 30 zuwa 40 duk wata saboda rashin biyansu hakkinsu.

Ya ce, "Mun mamaye gidan gwamnati ne kamar yadda muka yi alkawari kuma sai an biya mana bukatunmu kafin mu bar nan."

"Zamu cigaba da barci a nan tunda ma harda kayan shimfida muka zo."

"Na sanar da mutanena, ko matsuwa ce ta kamasu, su yi ta a nan saboda warin ya riski gwamnan. Babu inda zamu."

"Na bukaci ma'aikatan Karamar hukuma tun a watan Yuni da su bani kiyasin 'yan kungiyarmu da suka rasa rayukansu a cikin watanni 25 da gwamnati ta rike mana hakkinmu. Amma nasan muna rasa mutane 4 zuwa 5 duk sati, wanda jimillar hakan ne zai kai 30 zuwa 40 duk wata."

A yayin da shugaban kamashon fansho na jihar, Terna Ahuwa, yake jawabi ga tsoffin ma'aikatan, ya roke su da su kara hakuri da gwamnatin jihar.

Har a lokacin da muka samu rahoton nan, tsoffin ma'aikatan na nan a gidan gwamnati, wasu na kwance a titi, wasu kuma sunyi kungiya suna tattaunawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel