CASER ta na so Gwamnati ta dawo da ‘Yan Najeriya Mazauna Afrika ta Kudu

CASER ta na so Gwamnati ta dawo da ‘Yan Najeriya Mazauna Afrika ta Kudu

Kungiyar nan ta Citizens Advocacy for Social and Economic Rights watau CASER ta bukaci gwamnatin Najeriya ta nemi duka mutanen Najeriya da ke kasar Afrika ta Kudu su dawo gida.

A Ranar Talata, 3 ga Watan Satumba na 2019 ne CASER ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bukaci ‘Yan kasar nan su baro kasar Afrika ta Kudu. Shugaban wannan kungiya ne ya yi wannan kira.

Frank Tietie ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai jiya kamar yadda mu ka samu labari. Mista Tietie ya na ganin cewa lokaci ya yi da ‘Yan Najeriya za su tsira da ransu.

Shugaban CASER watau Frank Tietie ya ce: “Wannan mataki ya zama dole domin kare wadannan ‘Yan Najeriya da ke ci-rani a kasar Afrika ta Kudu daga fadawa cikin harin ‘yan gari a kasar wajen.”

KU KARANTA: An fara kone-kone a katin ShopRite da ke Najeriya

Mista Frank Tietie ya kara da cewa kasar Afrika ta Kudu ta yi sakaci wajen hana aukuwar wadannan munanan hare-hare ga ‘Yan Najeriya. Wannan ya sa ta nemi a dauki wani mataki.

A cewar Mista Tietie, ya kamata Najeriya ta hukunta kamfanonin kasar ta Afrika ta Kudu, bugu da kari shugaban na CASER ya yi kira ga ‘yan Najeriya su kauracewa duk kayan kasar wajen.

Wannan kira ya fara da a daina amfani da kamfanonin sadarwan kasar Kudancin Afrikan, a komawa na gida. An kuma nemi mutane su yi watsi da tashoshi gidan talabijin na kasar.

CASER ta ce: “Ministan shari’a ya fara shirya kara a kotu na karbar kudi daga hannun kasar ta Afrika domin wadanda aka kai wa farmaki su samu na rage zafi tare da hukunta masu lafi.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel