Ezeokafor: Gwamnati da ‘Yan Siyasa su shiryawa zanga-zangar ‘Yan Najeriya

Ezeokafor: Gwamnati da ‘Yan Siyasa su shiryawa zanga-zangar ‘Yan Najeriya

Limamin babban cocin Katolika na Mabiya addinin Kirista da ke babban birnin Awka na jihar Akwa Ibom, Rabaren Paulinus Ezeokafor, ya nemi gwamnati ta shiryawa zanga-zanga a Najeriya.

Wannan babban Malamin addinin Kirista ya ce jama’ar kasar nan za su yi bore nan gaba kadan. Malamin ya bayyana wannan ne lokacin da ya ke magana kan harin da aka kai wa Ike Ekweremadu.

Shehin ya yi wannan jawabi ne a cocin St. James da ke Garin Nneni a cikin karamar hukumar Anaocha da ke jihar Anambra. Ya ce dole ‘yan siyasa su kara kintsi ko koma su gamu da fushin ‘Yan Najeriya.

Paulinus Ezeokafor ya ce irin dukan da aka yi mataimakin shugaban majalisar dattawa na zuwa kan wasu manyan ‘yan siyasar idan har ba a kawo karshen wahalar da mutanen Najeriya su ke ciki ba a halin yanzu.

Wannan Limami ya ce tun ba yau ba ake jiran ranar da mutanen da yunwa ya galabaitar za su fara jibgar ‘yan siyasan kasar nan a dalilin irin mummunan shugabancin da ake gani. Shehin ya ce an saba haka a Duniya.

KU KARANTA: Ekweremadu ya nemi Najeriya ta datse dangantaka da Afrika ta Kudu

"'Yan Najeriya su na fama da yunwa da haushi. Ba za ka bugi yaro sannan ka hana sa kuka ba. Mutane kuma su na da damar yin zanga-zanga muddin ba su rike wani makami ba. Haka ake yi a ko ina.” Inji Malamin.

Bajimin Malamin ya ce kullum mutane mutuwa su ke yi a Najeriya saboda irin shugabancin da ake fama da shi. Paulinus Ezeokafor ya nemi ‘yan siyasa su yi kokarin da za su yi wajen kawo zaman lafiya a kasar.

Malamin da ya yi kaurin suna a Kudancin Najeriya ya kammala da cewa: “Babu hanyoyi masu kyau, babu magani a asibiti, babu wutar lantarki, rayuwa ta yi tsada. Amma mutane na cigaba da satar dukiyar kasa.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel