APC ta ci gaba da rike hukuncin dakatar da Abdulmumin Kofa

APC ta ci gaba da rike hukuncin dakatar da Abdulmumin Kofa

Jam'iyyar APC reshen jihar Kano, ta ci gaba da rike hukuncin da ta zartar na dakatar da dan majalisar tarayya mai wakilcin mazabar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, tare da neman uwar jam'iyyar ta kore gaba daya.

Jamiyyar APC reshen karamar hukumar Bebeji, ta dakatar da Kofa har na tsawon shekara daya biyo bayan zargin da ta ke masa na yi wa jam'iyyar zagon kasa.

A wata sanarwa da shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Bebeji, Suleiman Gwarmai, ya sanya wa hannu, ya ce an dakatar da dan majalisar ne biyo bayan hukuncin da kwamitin amintattu na mutum bakwai ya yanke kan zargin da ake masa.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwato, Alhaji Suleiman ya ce an dauki matakin ne bayan da kwamitin na mutum bakwai da jam'iyyar ta kafa ke ci gaba da bincike da tattaro rahotanni akan matakin karshe da za a dauka.

KARANTA KUMA: Onochie ta lissafa matakai 8 da gwamnatin tarayya ta dauka kan kin jinin 'yan Najeriya a Afirka ta Kudu

Sai dai a ranar Larabar da ta gabata, babban sakataren jam'iyyar APC na Kano, Ibrahim Sarina, ya ce za a ci gaba da rike wannan hukunci na dakaci da aka yi wa dan majalisar bayan da kwamitin amintattu ya gabatar da rahotonsa.

Ana iya tuna cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta kaddamar tare da tabbatar da nasarar dan majalisa Kofa, lamarin da ya zuwa yanzu ake ci gaba da kalubalanta a gaban kotu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel