EFCC ta kama madamfaran yanar gizo 60 a Akwa Ibom

EFCC ta kama madamfaran yanar gizo 60 a Akwa Ibom

Hukumar yaki da rashawa ta Najeriya EFCC a reshen ta na birnin Uyo, ta sanar da cewa ta cafke madanfaran yanar gizo guda sittin yayin da zartar da hukuncin kan miyagu 37 daga shekarar 2017 kawo wa yanzu.

Shugaban reshen hukumar, Mr Garba Dugum, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata cikin birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Dugum wanda ya wakilci mataimakin shugaban hukumar mai kula da yankin Kudancin Kudu, Alex Ebbah, ya ce EFCC na ci gaba da gudanar da binciken hadin gwiwa a tsakaninta da hukumar tsaro da binciken diddigi ta kasar Amurka, FBI.

Babu shakka hukumomin biyu da ke ci gaba da yakar masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, sun koka kan yadda zamba cikin aminci da kuma damfara ke karuwa ta intanet wato yanar gizo musamman a kasashen biyu.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati a reshen ta na jihar Kano, ta samu nasarar samo kimanin naira miliyan 798.5 a hannun miyagun mutane da suka aikata laifuka daban-daban a tsakanin watan Janairu zuwa Agusta na shekarar da muke ciki.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yaro a jihar Katsina

Shugaban hukumar EFCC reshen jihar Kano, ACP Akaninyene Ezima, wanda ya gana da manema labarai na jaridar The Nation a ranar Litinin da ta gabata, ya gabatar da jawabai na karin haske a kan sha'anin hukumar karkashin reshen da ya ke jagoranta.

Ya ce a halin yanzu akwai miyagu kimanin 280 da suka shiga hannu a wannan shekara sakamakon laifukan da suka aikata daban-daban masu nasaba da halasta kudade na haram.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel