Hajjin 2019: Mahajjata 28,612 sun dawo gida Najeriya a tashi 59 - NAHCON

Hajjin 2019: Mahajjata 28,612 sun dawo gida Najeriya a tashi 59 - NAHCON

Hukumar da ke kula da jin dadin mahajattan Najeriya (NAHCON), tace zuwa yanzu ta dawo da mahajatta 28,612 zuwa gida Najeriya a tashi 59.

A cewar hukumar da cibiyar da ke kula da hakan a Makkah a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba, mahajattan baya-bayan nan da suka dawo sun kasance su 531 daga jihar Kaduna tare da jami’an NAHCON biyu a cikin jirgin Max Air mai lamba NGL 2076.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa NAHCON ta yi jigilar alhazai 44,450 zuwa Saudiyya domin sauke farali daga hukumar jin dadin alhazai na jiha, a tashi 93.

Akalla alhazai 1.8 miliyan a fadin duniya, ciki harda yan Najeriya 65,000 ne suka yi aikin hajjin bana a kasa mai tsarki.

KU KARANTA KUMA: Zamu wallafa sunayen yan siyasan da yan damfara suka dauki nauyinsu wajen samun kujerar mulki – EFCC

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kungiya da ke lura da sha’anin aikin Hajji da Umrah a Duniya mai suna “Hajj and Umrah Forum” ta karrama gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Labarai24 ta rahoto cewa Sheikh Ibn Muhammad shi ne wanda ya ba gwamnan na Kano wani hatimin Al-Qur’ani mai dauke da rigar dakin Ka’aba mai tsarki a matsayin lambar yabo na musamman.

Ibn Muhammad ya ba Mai girma Abdullahi Ganduje wannan kyauta na karamci ne a madadin kungiyar ta Hajj and Umrah Forum saboda irin kokarin da gwamnatin jiharsa tayi wajen aikin hajjin bana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel