Ka janye alaka da Afrika ta Kudu yanzu – Sanata Ekweremadu ya fadawa Shugaba Buhari

Ka janye alaka da Afrika ta Kudu yanzu – Sanata Ekweremadu ya fadawa Shugaba Buhari

Mun ji cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa a Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yanke dangantakar da ke tsakaninta da kasar Afrika ta Kudu.

Sanata Ike Ekweremadu ya nemi Najeriya ta datse duk wata alaka ta kasa da kasa da ke tsakanin ta Afrika ta Kudu ne a dalilin sababbin harin da aka kai wa wasu ‘Yan Najeriya da ke kasar wajen.

Ike Ekweremadu ya yi Allah-wadai da harin da ake kai wa mutanen Najeriya a kasar ta Afrika ta Kudu. Ekweramadu ya ce akwai jahilci da rashin kishin Afrika da butulci a game da hare-haren.

Babban ‘Dan majalisar ya ke cewa: “Abin tada hankali ne ace har yanzu gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ba ta dauki wani mataki na kare rayukan ‘Yanuwanta Afrika musamman Najeriya ba.”

Sanatan ya ce farmakin da ake kai wa ‘Yan Najeriya abin tsoro ne kuma abin ya yi kamari don haka ya nemi gwamnatin Najeriya da sauran kasashen Afrika da kungiyar AU su dauki mataki.

KU KARANTA: An kai hari a wani shago a kan rikicin Najeriya da Afrika ta Kudu

Sanatan ya ce: “Dole kungiyar AU na kasashen Afrika ta tashi tsaye yanzu. AU za ta zama kwankwan banza idan har mutanen Afrika ba za su iya samun zaman lafiya a cikin kasashen Nahiyarsu ba.”

Ekweremadu ya ke cewa: “Ya kamata kungiyar AU ta kira wani taron gaggawa domin ta hukunta kasar Afrika ta Kudu; ta kuma dakatar da ita daga kungiyar saboda harin da ta ke kai wa ‘Yanuwanta.”

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya koka da yadda Kasar Kudancin Afrika ta ke sakawa mutanen da su ka yi ruwa da tsaki wajen ganin ta kai matakin da ta kai a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel