Zargin badakala: Dan takarar shugaban kasa ya nemi miliyan N500 a hannun EFCC

Zargin badakala: Dan takarar shugaban kasa ya nemi miliyan N500 a hannun EFCC

A ranar Talata ne hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta sanar da wata babbar kotu dake Abuja cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar HDP, Ambrose Owuru, ya dade a cikin jerin sunayen mutanen da take tuhuma da tafka badakalar kudi.

Hukumar EFCC ta ce har yanzu maganar tuhumar Owuru da badakala tana gaban reshen babbar kotun tarayya dake Fatakwal a jihar Ribas.

Lauyan EFCC, Ibrahim Audu, ne ya bayyana wa kotu hakan bayan ya wakilci hukumar a karar da Mista Owuru ya shigar a kan hallacci bayyana nemansa ruwa a jallo da hukumar EFCC ta yi a shafukan jarida ranar 10 ga watan Yuli, 2018.

Mista Audu ya sanar da alkalin kotun, Jastis Nkeonye Maha, cewa Mista Owuru ya shiga wasan buya da hukumar EFCC, lamarin da yasa kotun Fatakwal ta bayar da takardar umarnin a kama shi.

Lauyan ya ce EFCC na tuhumar Mista Owuru da laifin yin karya domin karbar kudi a wani cinikin fili.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa a ranar 7 ga watan Agusta ne lauyan da ya wakilci Mista Owuru, Mista Eze Nnayenlugo, ya sanar da kotu cewa EFCC na tuhumar Mista Owuru da laifin tafka badakala bayan a zahirin gaskiya magana ce ta 'cinikin fili'.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Majalisar dinkin duniya ta yi kira a kan a gaggauta kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Da aka dawo zaman kotun ranar Talata, lauyan Mista Owuru, Chukwunoyerem Njoku, ya roki kotun ta amince da bukatun wanda yake kare wa da suka hada da biyan shi diyyar miliyan N500 sakamakon bata masa suna da suka y ta hanyar bayyana nemansa ruwa a jallo a shafukan jarida.

Kazalika, ya roki kotun ta dakatar da hukumar EFCC daga kara wallafa neman Mista Owuru a shafukan jarida.

Njoku ya bayyana cewa hukumar EFCC bata da ikon bayyana neman wani mutum 'ruwa a jallo' ba tare da samun izinin yin hakan daga kotu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel