Buhari zai shilla kasar Afirka ta kudu don dakatar da kisan da ake yi ma yan Najeriya

Buhari zai shilla kasar Afirka ta kudu don dakatar da kisan da ake yi ma yan Najeriya

Shirye shirye sun yi nisa game da tafiyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi zuwa kasar Afirka ta kudu domin kawo karshen hare haren da yan kasar suke kaiwa yan Najeriya, wanda yayi sanadiyyar mutuwar da dama tare da asarar arzikinsu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito ana sa ran Buhari zai yi wannan tattaki ne a watan gobe, inda zai tattauna da shugaban kasar Afirka ta kudu da sauran mahukuntar kasar game da wannan cin zarafi da yan kasarsu suke yi ma baki.

KU KARANTA: Yadda na zama jagoran yan kwallon kungiyar Super Eagles – Ahmed Musa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sanarwar da ta fito daga ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Afirka ta kudu ta yi kira ga shugaban kasar, Cyril Ramaphosa daya kawo karshen wannan matsalar, saboda Najeriya ba za ta lamunta ba.

Shi ma jakadan Najeriya a Afirka ta kudu, Kabiru Bala ya baiwa yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu tabbacin samun tallafin daya kamata daga ofisoshin jakadancin Najeriya dake Johannesburg da Pretoria.

“Muna kira ga dukkanin yan Najeriya da wadannan hare hare suka shafa dasu garzayo zuwa ofishin jakadancinmu su bada bayanin halin da suke ciki, dukkanin ofisoshinmu guda biyu za su cigaba da maraba da yan Najeriya a wannan matsanancin hali da suke ciki.” Inji shi.

Haka zalika ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Geofferey Onyeama ya gayyaci jakadan kasar Afirka ta kudu a Najeriya domin su tattauna batun a babban birnin tarayya Abuja, sai dai rahotanni sun ruwaito jakadan yana cewa ba harin kin baki bane, suna kallon lamarin a matsayin harin ta’addanci ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel