Matatar man fetur ta kasa ta fara gangamin canje-canjen wajen aiki ga manajojinta

Matatar man fetur ta kasa ta fara gangamin canje-canjen wajen aiki ga manajojinta

- Matatar man fetur ta kasa ta fara gangamin canzawa manajojinta wajen aiki

- Hakan ya biyo bayan alkawarin da sabon babban shugaban kamfanin yayi na tsaftace da gyara matatar

- Mele Kyari, yayi alakwarin ba zai lamunci almundahana ba komai kankantar ta, hakan zai dawo da martabar matatar nan ba da dadewa ba

Wata majiya, makusanciya ga matatar man fetur na kasa NNPC ta sanar da Premium Times a ranar Litinin a kan manajoji 15 da abin ya shafa.

Duk da Hukumar matatar ba ta nemi shawarar yin hakan ba, majiyarmu da ta bukaci a boye sunanta tace hakan ya biyo bayan alkawarin da sabon babban manajan matatar ya dauka, Mele Kyari, na gyara da saiti ga babbar matatar man fetur din ta kasa.

Kyari ya tabbatar da cigaban ga Premium Times a wayar da su kayi ranar Talata.

DUBA WANNAN: Tsohon shugaban kasar Sudan ya bayyana inda ya samo makuden kudaden da aka kama a gidansa

"Eh hakane, gyaran da nayi alkawari ne aka fara," Kyari ya tabbatar.

"Canje-canjen manajojin abu ne da dole in hanzarta yi don dawo da martabar wajen. Abun dubawa anan shine nagartarmu na yin kasa, don haka dole ne in dawo da ita. Wasu sun maida gurin, wajen neman kwangila. A don haka ne na ga dole in tsayar da hakan kuma in farfado da wajen don cimma burin kasarmu."

Majiyarmu ta ce akwai yuwuwar canjin ya kai ga duk bangarorin matatar da rassanta da ke fadin kasar nan.

"An fara sharar, yanzu ma aka fara. Za ta cigaba kuma har kananan bangarorin matatar za ta kai." Inji majiyarmu.

"Amfanin gyare-gyaren shine kawo cigaba ga aiyukan NPDC don ganin ta kai ga sauke nauyinta. Sabon shugabancin matatar ta shirya gyaran da zai tabbatar da kowanne ma'aikaci ya sauke nauyinsa."

Majiyarmu bata samu damar samun sunayen manajojin da abin ya shafa ba amma akwai yuwuwar matatar ta sanar da kanta nan ba da dadewa ba.

Majiyarmu tace sabon cigaban zai kawo sabbin dabaru da cigaba don toshe baraka da kuma karo kudin shiga kamar yadda sabon babban manajan ya ke buri.

Kyari ya kara da cewa ba zai lamunci almundahana ta kudade ba komai kankantar ta, da kuma burin tsaftace babbar matatar, har ma da kananan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel