Xenophobia: 'Yan Najeriya za su kauracewa sayan kayayyakin kasar Afirka ta Kudu

Xenophobia: 'Yan Najeriya za su kauracewa sayan kayayyakin kasar Afirka ta Kudu

Biyo bayan ci gaba da kai farmaki da munanan hare-hare na kin jinin al'ummar Najeriya da kuma harkokin kasuwancin su a kasar Afirka ta Kudu, wasu daga cikin al'ummar kasar nan sun nemi da a kauracewa duk wata harkar cinikayya ta makociyar kasar.

Musamman mazauna babban birnin kasar nan na tarayya wato Abuja, 'yan Najeriya da dama yayin ganawa da manema labarai na jaridar Daily Trust, sun bayyana ra'ayoyin su kan dakile duk wata harkar cinikayya da kasar Afirka ta Kudu, lamarin da suka ce wata dangartaka ta zumunci da ke tsakanin kasashen biyu ta yanke a yanzu.

Babu shakka 'yan Najeriya da dama sun jima suna kace-nace da kiraye-kiraye kan kauracewa amfani da dukkanin kayayyakin kasuwancin kasar Afirka ta Kudu a sanadiyar kin jinin da wasu 'yan kasar ke nuna wa 'yan Najeriya da 'yan wasu kasashen da ke zama a can.

Akwai kamfanonin Afirka ta Kudu da ke ci gaba da cin moriyar arziki a Najeriya musamman babban kamfanin nan na sadarwa wato MTN da kuma shagunan saye da sayarwa da ke wasu manyan birane a Najeriya na Shoprite da kuma kamfanin talabijin na DSTV.

'Yan Najeriya da dama ba su gushe ba wajen ci gaba da kiraye-kiraye musamman a zaurukan sada zumunta na Twitter da Facebook, inda suke bayyana takaici kan yadda wadannan kamfanonin mallakin kasar Afrika Ta Kudu ke samun arziki da 'yan Najeriya, amma wasu 'yan kasar ke nuna kin jini da kuma kai hari kan 'yan Najeriya mazauna can.

KARANTA KUMA: Taron Ilimi: Osinbajo ya ziyarci jihar Kano

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, tuni dai gwamnatin Najeriya ta aike wa jakadan Afirka Ta Kudu a kasar sammaci kan hare-haren kin jinin baki da ake kai wa 'yan Najeriya a kasar.

Haka zalika, ministan harkokin kasashen ketare, Mr Geoffrey Onyeama, zai gana da jakadan Afirka Ta Kudu a ranar Talata kan kashe-kashe na baya-bayan nan da aka fara a karshen makon nan.

Mr Geoffrey Onyeama ya ce gwamnatin Najeriya za ta dauki kwararan matakai kan harin da aka kai wa 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu a ranar Litinin, lamarin da ya ce ba za ta sabu domin kuwa da zafi-zafi ake dukan karfe.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel