CBN ta umarci jama’a su cigaba da kai tsofaffin kudi banki kafin ranar karshe

CBN ta umarci jama’a su cigaba da kai tsofaffin kudi banki kafin ranar karshe

Babban bankin Najeriya ta yi kira ga yan Najeriya dasu cigaba da kai tsofaffin kudadensu tare da yagaggu zuwa ga bankuna mafi kusa domin samun canjin sababbin kudade har zuwa ranar 2 ga watan Satumba, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito daraktan watsa labaru na CBN, Isaac Okoroafor ne ya bayyana haka, inda ya nemi jama’a su cigaba da kai tsofaffin kudadensu bankuna duk da cikar wa’adin ranar 2 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Kishin-kishin: An kashe wanda su ka sace ‘Dan Majalisar Zariya

Kaakakin bankin ya bayyana cewa wa’adin ranar 2 ga watan Satumba bai shafi jama’a gama gari ba, illa bankunan dake hulda da babban bankin, su ne aka sanya musu wannan rana domin tantance tsofaffin kudaden da suka amsa.

“Jama’a su cigaba da mika tsofaffin kudadensu ga bankuna har bayan cikar wa’adin 1 ga watan Satumba, wa’adin bai shafi jama’an dake kai tsofaffin kudadensu bankuna ba, illa bankuna, su wannan wa’adi ya shafa.

“Saboda daga wannan rana CBN ba za ta sake tantance musu tsofaffin kudaden da suka kawo mata a kyauta ba, tun daga 3 ga watan Yuni muka fara karban tsofaffin kudade daga bankuna, muna kuma tantance musu ba tare da cajesu ko sisi ba.

“Amma daga ranar 2 ga watan Satumba za mu daina tantance musu tsofaffin kudaden da za su kawo mana a kyauta, har sai mun cajesu wani abu, ko kuma su tantance da kansu tun kafin su kawo mana.” Inji shi.

Daga karshe, Isaac yace batun kai tsofaffin kudade bankuna da jama’a ke yi abu ne wanda zai cigaba kamar dai yadda aka saba a kullum, don haka kada kowa ya damu da wa’adin ranar 2 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel