Rashin Tsaro: Sufeto Janar na 'yan sanda ya koma Kudu maso Yammacin Najeriya
A yayin da lamari na rashin tsaro ya ci tura a kasar inda babu wani yanki da bai addaba ba, jaridar The Nation ta ruwaito cewa, babban sufeton 'yan sandan Najeriya, Muhammadu Adamu, zai shafe wannan mako a yankin Kudu maso Yammacin kasar.
Biyo bayan wannan sauyin sheka, babban sufeton na 'yan sanda zai tumke damarar shirye-shiryensa ta bayar da tsaro da kuma aminci a yankin wanda ke fama da ta'addancin masu garkuwa da mutane da kuma sauran ababe masu barazana da zaman lafiya.
Tun a ranar Alhamis da ta gabata ne, sufeton na 'yan sanda ya bayar da umarnin tura jirage masu saukar Ungulu wato helikwafta, domin su dawwama kan aikin sintiri da kai komo a yankin Kudu maso Yamma da kuma na Arewa maso Yamma.
Jiragen za su rika sintiri a sararin samaniyar manyan hanyoyi da kuma dajika inda kashe-kashe da kuma masu garkuwa da mutane gami da karbar kudin fansa ke cin karen su babu babbaka.
A tsawon mako guda da babban sufeton na 'yan sanda zai shafe a yankin bayan da ya sauka a birnin Ibadan na jihar Oyo a daren jiya na Lahadi, zai kaddamar da sabbin tsare-tsare na tabbatar da tsaro a yayin taron masu ruwa da tsaki da za a gudanar a yau Litinin cikin babban dakin taro na ICC da ke jami'ar Ibadan.
Rahotanni sun bayyana cewa, babban sufeton na kasa zai kaddamar da sabbin tsare-tsare kan yadda za a tunkari kalubale na rashin tsaro a jihohin Oyo, Osun, Ondo, Ogun, Legas da kuma Ekiti, a yayin taron da gwamnonin jihohin za su halarta a lokuta daban-daban.
KARANTA KUMA: Buhari ba ya da maganin rashin tsaro a Najeriya - PDP
Kazalika babban jami'in tsaron zai kai ziyarar gani da ido kan wasu gine-gine tare da ganawa da jami'an tsaro a jihar Oyo gabanin ziyartar gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola.
Babban sufeton zai kuma kasance a jihohin Ekiti da Ondo a ranar Alhamis, yayin da zai dira birnin Ikko wato Legas da kuma Ogun a ranar Juma'a.
Ana kuma sa ran Sufeto Adamu zai gana a lokuta mabambanta juna da sarakunan gargajiya na yankin Kudu maso Yamma.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng