Shugaba Buhari ya shirya tsaf don kawo karshen tsaikon biyan maqudan kudin da ake baiwa masu ritaya

Shugaba Buhari ya shirya tsaf don kawo karshen tsaikon biyan maqudan kudin da ake baiwa masu ritaya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya tsaf don kawo karshen tsaikon da ake samu wajen biyan maqudan kudin ritaya

- Shugaban ya umarci ministar kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed da ta shirya tare da sakin naira biliyan 62.83 don fidda hakkin masu ritaya

- Ya kuma umarta da a hada da hakkokin na masu ritaya a kasafin kudi na shekaru uku masu zuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara shirye-shiryen kawo karshen jinkirin biyan makudan kudaden da gwamnati ke biyan masu ritaya.

Shugaban kasar ya umarci ministan kudi, kasafin kudi da tsare tsare Zainab Ahmed, da ta gyara tare da sakin naira biliyan 62.83 don fidda hakkin fansho na masu ritayar.

A wata wasikar da shugaban ma'aikata na tarayya, Abba Kyari yasa hannu, an umarci ofishin kasafin kudi na tarayya da su hada naira biliyan 12.83 na shekarar 2020, naira biliyan 25 na shekara 2021 da naira biliyan 25 na shekarar 2022 don biyan fansho ga ma'aikatan gwamnatin tarayya.

DUBA WANNAN: Shugaban karamar hukuma ya yi alkawarin daukar nauyin jaririyar da mahaifiyarta tayi yunkurin siyar da ita

Shugaban kasar, ya kara da umartar ministar kudin ta tabbatar da sakin kudin gabadaya bayan hukumomin da yakamata sun amince.

Wannan cigaban na nuna cewa ana gujewa abinda ya faru ne a shekarar 2017 na nakasu da aka samu a kasafin kudin biyan masu ritayar har na Naira biliyan 62.83.

Tsaikon yaci karo da dokan fansho da aka gyara a shekarar 2014, wadda tace in dai ma'aikaci yayi ritaya a shekara 50 ko sama da haka, a take yana da damar more kudin da ya adana na ritayarshi.

Dokar ta kara da cewa, idan ma'akaci yayi ritaya kafin shekaru 50 saboda matsalar kwakwalwa ko nakasa, ko kuma saboda dokar aikinshi, to a take yana da damar morar abinda ya tara.

Amma idan ma'akaci ya rasa aikinsa da gangan kafin shekaru 50, toh zai iya morar abinda ya tara ne bayan wata 6 da ritayar, matukar bai samu wani aikin ba.

Kokarin da kamashon fansho ta kasa tayi don fitar da hakkin masu ritayar yaci tura, amma da alamar wadanda abin ya faru da su, farinciki zai cikasu da jin umarnin Shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel