Daga karshe: Hukumar kwastam ta yi magana a kan rufe iyakokin Najeriya

Daga karshe: Hukumar kwastam ta yi magana a kan rufe iyakokin Najeriya

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS), wacce aka fi kira da 'Kwastam', ta bayar da umarnin rufe iyakokin Najeriya da ke jihohin arewa ta tsakiya.

Umarnin rufe iyakokin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin shugaban hukumar kwastam, MA Dahiru.

An aika takardar umarnin rufe iyakokin ne zuwa shugabannin ofisoshin hukumar kwastam da ke jihohin Kwara, Kogi da Neja.

"Kamar yadda takardar sanarwar EII mai lamba 020 ta umarce ku, na rubuto wannan wasika domin yi tuna muku cewa ku tabbatar an rufe dukkan iyakokin Najeriya da ke karkashin ikon ku," a cewar takardar.

Umarnin rufe iyakokin ya fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Agusta.

"Rufe iyakokin ya shafi duk wata hada-hadar kaya da zirga-zirgar mutane," takardar ta bayyana.

A cikin makon jiya ne rufe iyakar Najeriya da Kotono da ke Seme a Legas ya ritsa da mutane da dama da ke harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

DUBA WANNAN: Buhari ya sallami babban sakataren hukumar NCPC, ya maye gurbinsa

Amma da aka tuntubi Joseph Attah, kakakin hukumar kwastam, ya musanta rufe iyakokin.

"Ba a rufe iyakokin Najeriya ba," a cewar sa.

"Mu na gudanar da wasu aiyuka ne tare da hadin gwuiwar sauran jami'an tsaro domin magance aiyukan wasu bata gari," a cewar Attah.

A wani jawabi da ya fitar a baya, Attah ya bayyana cewa aikin zai shafi motsin jama'a da kayayyaki a sassan Najeriya.

Da yake kira ga jama'a a kan kar su damu, Attah ya bayyana cewa sun kirkiri aikin ne saboda dalilan tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel