Minista Godswill Akpabio ya yi damarar ceto mutanen Neja-Delta daga kangi

Minista Godswill Akpabio ya yi damarar ceto mutanen Neja-Delta daga kangi

Babban Ministan harkokin Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio ya fito ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta duba lamarin mutanen Kudu maso Kudu.

Sabon Ministan na Najeriya ya ke cewa sun fara hangen yadda za a kawowa mutanen yankin Neja-Delta sauyi a rayuwar su tare da kuma gina abubuwan more rayuwa a wannan bangare na kasar.

Akpabio ya ke cewa a matsayinsa na wanda ya fito daga cikin sashen Neja-Delta a Kudancin kasar, zai yi kokarin ganin sun bar wani tarihin da za a rika tunawa da su na tsawon lokaci a Najeriya.

A wajen wani zama da Godswill Akpabio ya yi da Matasan da ke kokarin ganin cigaban yankin na Neja-Delta ne ya bayyana wannan. Wadannan Matasa sun ziyarci sabon Ministan ne a ofishinsa kwanan nan.

KU KARANTA: Ministan wasanni: Dole mu dama da Matasa domin gaba ta yi kyau

Akpabio ya ke cewa: “Shugaban kasa a shirya ya ke da ya canza fuskar Yankin (Neja-Delta). Ina bukatar ku tafi ku fadawa mutanen da ke gida cewa yanzu lokacin kuka da shan wahala ya zo karshe.”

Kafin nan Godswill Akabio ya rantse ba za su bada kunya ba. Akpabio ya sake godewa shugaba Buhari da ya ba shi wannan kujera inda ya ce zai yi aiki tukuru tare da Festus Keyamo da Ita Enang.

Festus Keyamo shi ne wanda zai taimakawa tsohon gwamnan na Akwa-Ibom wajen rike ma’aikatar Neja-Deltan. Ita Enang kuma shi ne ya zama Mai ba Buhari shawara kan harkokin yankin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel