Kwastam ta bayar da cikakken bayani akan manyan motocin yaki 6 da aka kama a Adamawa

Kwastam ta bayar da cikakken bayani akan manyan motocin yaki 6 da aka kama a Adamawa

Hukumar Kwastam na Najeriya a ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta, ta bayyana cewa matocin yaki na sojoji da hukumomin Najeriya ta kama kwanan nan na jumhuriyar Nijar ne.

Joseph Attah, kakakin hukumar Kwastam, ya bayyana cewa hukumomin Najeriya ta kuma damke direbobi shida da ke tuka motocin.

A kwanan nan ne rundunar sojin Najeriya a jihar Adamawa ta damke wasu manyan motocin yaki masu sile sannan ta mika su ga hukumar Kwastam a ranar Asabar.

An shigo da manyan motocin ne ba tare da takardun da suka kamata ba, ciki harda na mallakatsu, daga inda suka fito da kuma inda za su, lokaacin da sojojin Najeriya suka kwace su a karamar hukumar Fufore.

Daga bisani saai aka damka su zuwa ga hukumar kwastam a wani taro da aka gudanar a Konkol, jihar Adamawa.

Majiyoyi na sujoji sun bayyana cewa akwai alamar tambaya akan yadda aka shigo da motocin, musamman a wani yanki da ke fama da ta’addanci har na tsawo shekara 10.

Adamawa, Borno da Yobe, sune jihohi uku da suka fi fuskantar annobar Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Ruwan sama mai karfi ya lalata gidaje 100 a mahaifar Buhari

Mista Attah yace direbobin da ke tukin motocin sun bayyana cewa sun baro Kamaru sannan suna a hanyarsu ta zuwa jumhuriyar Nijar ne.

Yace an bukaci hukumar Kwastam ta karbi ragamar kayayyakin domin tana da ikon yin haka akan duk wani abu da ya ketaro ta iyakar Najeriya.

Rundunar soji da ta SSS basu fitar da jawabi akan kayayyakin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel