Yanzu Yanzu: Kasar Saudiyya za ta hukunta yan Najeria 23 (jerin sunaye)

Yanzu Yanzu: Kasar Saudiyya za ta hukunta yan Najeria 23 (jerin sunaye)

Rahotanni sun kawo cewa kasar Saudiyya za ta hukunta yan Najeriya 23 daga yanzu zuwa kowani lokaci, akan laifufukan da suka shafi miyagun kwayoyi. An kama su da laifin safarar miyagun kwayoyi wanda hukuncinsa kisan kai ne.

An kama su ne tsakanin 2016 da 2017 a filin jirgin sama Sari Abdul-Aziz, da ke Jeddah da kuma filin jirgin sama na Yarima Muhammad bin Abdu-Aziz, Madinah bayan an same su dauke da haratattun kayayyaki, takardar kasar Saudiyya ta bayyana.

KU KARANTA KUMA: Hamisu Wadume: Yan siyasa nike yima aiki, APC ta bani N13m a zaben 2019

Ga sunayensu a kasa:

1. Adeniyi Adebayo Zikri

2. Tunde Ibrahim

3. Jimoh Idhola Lawal

4. Lolo Babatunde

5. Sulaiman Tunde

6. Idris Adewuumi Adepoju

7. Abdul Raimi Awela

8. Ajibola Yusuf Makeen Ajiboye

9. Adam Idris Abubakar

10. Saka Zakaria

11. Biola Lawal

12. Isa Abubakar Adam

13. Ibrahim Chiroma

14. Hafis Amosu

15. Aliu Muhammad Funmilayo

16. Omoyemi Bishi

17. Mistura Yekini

18. Amina Ajoke Alobi

19. Kuburat Ibrahim

20. Alaja Olufunke Alalaoe Abdulqadir

21. Fawsat Balagun Alabi

22. Aisha Muhammad Amira

23. Adebayo Zakariya.

Hakan na zuwa ne yan makonni bayan huumomin Saudiyya sun hukunta Kudirat Afolabi akan safarar migayun kwayoyi da Saheed Sobade, wani dan Najeriya da aka kama da hodar iblis gram 1, 183 a Jeddah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel