Mafi karancin albashi: Maganar ta dawo bisa teburin Buhari

Mafi karancin albashi: Maganar ta dawo bisa teburin Buhari

-Tattaunawar gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago a ranar Juma'a ta tashi ba tare da matsaya guda ba

-An daga wannan tattaunawar har zuwa 4 ga watan gobe inda ake sauraron abinda Shugaba Buhari zai fadi game da matsayar bangarorin biyu mabambanta

Ma’aikatan Najeriya za su sake wani sabon zaman jiran ranar da gwamnati za ta soma biyansu sabon mafi karancin albashi, a yayinda tattaunawa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya ta tashi baram-baram ranar Juma’a.

Kungiyar ‘yan kwadago da gwamnatin Najeriya sun shiga wata tattaunawa a ranar Juma’a domin dinke bakin matsalar da shafi mafi karancin albashi da Shugaba Buhari ya rattabawa hannu tun ranar 18 ga watan Afrilu.

KU KARANTA:Ruga: Tsarin ruga zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma, inji Matawalle

Tattaunawar wadda aka gudanar a ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya ta samu halartar ministan kwadago, babban sakataren ma’aikatar kudin Najeriya da kuma wakilin hukumar albashin ta kasa.

Wakilin jaridar The Nation ya shaida mana cewa bangarorin biyu sun tsaya a kan batun za su koma gaban Shugaba Buhari domin fada masa inda tattaunawar ta su ta tsaya kana kuma su dawo ranar 4 ga watan Satumba domin cigaba da ganawar.

Wata majiyar wadda ke da kusanci ga fadar Shugaban kasa ta ce an daga tattaunawar ne zuwa 4 ga watan Satumba domin a ba wa Shugaba Buhari lokaci isasshe domin ya duba wannan matsala ta mafi karancin albashi.

Dukkanin bangarorin biyu kowa ya toge a bisa bukatunsa, gwamnati na fadin abu daban haka suma ‘yan kwadago abu na daban suke fadi.

Kungiyar kwadago na bukatar karin 30% ga ma’aikatan dake a matakin lebul 07 zuwa 14 da kuma karin 25% ga albashin ma’aikatan dake matakin lebul 15 zuwa 17. Yayin da gwamnati ta tsaya a kan karin 9.5% da 5% ga matakan guda biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel