Da duminsa: Buhari ya amince da bawa gidajen talabijin da rediyo na intanet lasisi

Da duminsa: Buhari ya amince da bawa gidajen talabijin da rediyo na intanet lasisi

Shugaba Muhamadu Buhari ya bayar da umurnin yin wasu sauye-sauye a fanin watsa labarai ciki har a bayar da lasisin aiki ga wasu kafafen gidajen rediyo da talabijin da su rika watsa labaransu ta kafar intanet.

A cewar wata sanarwa da ta fito daga bakin Mr Segun Adeyemi, hadimin Ministan Labarai da Al'adu, sauye-sauyen za su inganta ayyuka a fanin ta watsa labarai.

Sanarwar ta ce, Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyanawa mambobin Kungiyoyin Masu Watsa Labarai na Najeriya (BON) a ranar Juma'a a Abuja yayin da suka kai masa ziyara cewa shugaban kasar ya amince da yi wa dokar watsa labarai garambawul.

DUBA WANNAN: Kotu: Ganduje ya gabatar da shaida mai katin zabe na bogi

Mohammed ya ce, "Ina son in sanar da ku cewa Shugaban kasa ya amince da yi wa dokar watsa labarai garambawul wadda hakan zai magance matsaloli da yawa da kuke korafi a kai.

"Shugaban kasar kuma ya amince da bayar da lasisin gidajen talabijin da rediyo na intanet ciki har da tashoshin kasashen waje da za su rika watsa shirye-shiryensu a Najeriya amma lasisin zai tabbatar da an bi tsari a harkar.

"Shugaban kasar kuma ya amince da wasu sauye-sauye masu yawa a fanin watsa labarai da zan sanar da ku a lokacin da ya dace."

Ministan ya yi alkawarin aiki tare da mambobin kungiyar ta BON yayin gudanar da garambawul ga dokokin aikin watsa labarai a kasar inda ya sake jadada kokarin gwamnati mai ci yanzu na bawa 'yan jarida damar yin aikinsu ba tare da tsangwama ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel