APC za ta yi mulkin Najeriya har bayan 2023, in ji Oshiomhole

APC za ta yi mulkin Najeriya har bayan 2023, in ji Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ya nuna karfin gwiwar cewa jam’iyyar za ta ci gaba da mulkin kasar har bayan cikar wa’adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu a 2023.

Da yake magana a wani taron ganawa da gwamnonin jam’iyyar, Oshiomhole yayi kira ga hadin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar domin ci gaban jam’iyyar da kasar.

Yayinda yake jadadda cewar aikin jagorancin jam’iyyar ya kasance da yan kalubale,Oshiomhole yace: “ya kasance kalubale a gare ni. Nayi kokarin hada kaina a matsayin gwamna da yanzu a matsayin Shugaban jam’iyya, faraway daga zabukan fidda gwani da kuma magance matsalolin tarurukan baya. Sannan zuwaa ga gudanar da zabe.”

Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya jagoranci tawagar gwamnonin zuwa wajen taron.

Gwamnonin da suka hallara sun hada da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da mataimakin gwamnan jihar Yobe, Idi Barde Gubana.

Ganawar wanda aka gudanar cikin sirri ya shafe tsawon sa’o’i biyu.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen Yan Najeriya 80 da aka kama da zambar miliyoyin daloli a kasar Amurka

Amma daga jam’iyyar har gwamnonin basu bayyana sakamakon ganawar ba.

Sai dai ana hasashen cewa an tattauna batun rikicin da ake fama dashi a jam’iyyar, da kuma bukatar yin sulhu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel