Yanzu-yanzu: Buhari zai shilla kasar Japan, zai halarci taron TICAD7

Yanzu-yanzu: Buhari zai shilla kasar Japan, zai halarci taron TICAD7

A ranar Lahadi, 25 ga wtaan Agusta shugaba Muhammadu Buhari zai shilla kasar Japan domin halartan taron hadakar kasar Asiyan da nahiyar Afrika inda zai kwashe mako daya kafin ya dawo ranar 31 ga wata.

Wannan ya bayyana a jawabin fadar shugaban kasa da ta saki da yammacin Juma'a inda ta ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja ranar Lahadi zuwa Japan domin halartan taron gagamin alakar Japan da cigabar Afirka a birnin Yokohama tsakanin 28 da 30 na watan Agusta, 2019."

Wannan shine karo na biyu da shugaba Buhari zai halarci taron TICAD6 a Nairobi, Kenya a Agustan 2016.

Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi inda zai yi magana kan alakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Japan da kuma abubuwa da Najeriya ta amfana a taron bara TICAD6."

KU KARANTA: Ban damu da hukuncin kotu ba, gwamna zan zama - Sanata Dino Melaye

"Bayan ganawar diflomassiyya da firam ministan Japa, Abe, shugaban kasa zai gana da wasu yan kasuwa da zasu sanya hannun jari a Najeriya."

Daga cikin wadanda zasu takawa Buhari baya sune gwamna Babagana Zulum, AbdulRahman AbdulRazaq, da Babajide Sanwoolo na jihohin Borno, Kwara da Kegas a jere; tare da ministoci da wasu manyan jami'an gwamnati."

Shugaban kasan zai dawo Najeriya ranar 31 ga Agusta, 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel