Ke duniya: Mutanen da suka je taimakon wanda mota ta buge, sun sace kudin jikinsa karkaf sun barshi cikin jini

Ke duniya: Mutanen da suka je taimakon wanda mota ta buge, sun sace kudin jikinsa karkaf sun barshi cikin jini

- Wani mutumi da mota ta buge sanadiyyar ficewar tayar motar ya fadi akan babbar hanyar Ikorodu dake jihar Legas

- Wannan dalili ne yasa mutane suka dunguma domin taimaka masa wajen dauke shi daga kan babbar hanyar wacce motoci ke ta faman kai kawo

- A wannan hali da mutumin ke ciki aka samu wani mai karfin hali ya zira hannu cikin rigarsa ya sace masa 'yan kudadensa

Wani matashin saurayi da hatsarin mota ya ritsa dashi a Ikorodu dake jihar Legas ya bayyana cewa mutanen da suka je domin su taimakesu sun sace mishi kudin dake cikin aljihunshi.

A yadda rahoton ya nuna, hatsarin ya faru ne yayin da tayar mota ta cire taje ta bige wani mutumi a lokacin da yake tafiya akan babur.

Wannan dalili ne yasa mutane suka yi dafifi domin su dauke daga kan babbar hanyar wacce motoci ke faman kai kawo, amma kuma a yayin da mutanen ke kokarin dauke mutumin, wani da ba a san ko waye ba ya sanya hannunsa a cikin aljihunshi ya dauke mishi kudi kimaninm naira dubu takwas.

KU KARANTA: Tirkashi: Aisha Idris ta fara tona asiri gami da bayyana sakonnin sirri da Afakallahu ya aikata mata

Wannan lamari dai bai yiwa mutumin dadi ba, domin kuwa duk da irin ciwon da yaji bai sa barawon ya tausaya masa ba, ya sakaya hannu ya zare masa dan kudin da yake riritawa.

Wannan abu da ya faru ba shine na farko ba, saboda ya sha faruwa a lokuta da dama idan hatsari makamancin haka ya faru a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel