Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta soke nasararar Dino Melaye a matsayin sanatan Kogi ta yamma

Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta soke nasararar Dino Melaye a matsayin sanatan Kogi ta yamma

Kotun sauraron korafin zaben majalisar dokokin tarayya da na jiha a Kogi ta soke nasarar zaben Sanata Dino Melaye mai wakiltan yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawa.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Dino a matsayin wanda ya lashe zaben sanata da aka gudanar a watan Fabrairu, amma sai Sanata Smart Adeyemi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya tunkari kotun zaben domin kalubalantar lamarin.

Smart ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai a zaben da suka hada da magudi, yawan kuri’u da suka wuce ka’ida da kuma rashin bin dokar zabe.

Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Justis A. O. Chijioke a wani hukunci da suka zartar a ranar Juma’a, 23 ga watan Agusta sun amince da hujojjin da Smart ya kafa inda suka yi umurnin sake zabe a yankin.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Magoya bayan Uche Nwosu sun lakada wa jami’an DSS dukan tsiya

A wani lamarin kuma, mun ji cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano na Jam'iyyar APC ya fara kare kansa a gaban kotun sauraron karar zaben gwamna a jihar Kano inda ya gabatar da shaidan baka da wasu takardu sai dai an gano shaidan yana dauke da katin zabe na bogi ne.

Idan ba a manta ba kotun na sauraron karar da jam'iyyar PDP da dan takarar gwamnan ta Abba Kabir Yusuf ya shigar ne na kallubalantar nasarar Ganduje a zaben gwamna da aka gudanar a Maris din 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel