Boko Haram: ‘Yan gudun hijira 133 sun dawo Najeriya daga kasar Kamaru

Boko Haram: ‘Yan gudun hijira 133 sun dawo Najeriya daga kasar Kamaru

Kimanin mutum 133 wadanda su kayi gudun hijira zuwa kasar Kamaru sakamakon rikicin Boko Haram sun dawo Najeriya a ranar Alhamis.

Wadannan mutanen na daga cikin ‘yan gudun hijira sama da miliyan biyu da rikicin Boko Haram ya watsa zuwa wurare da dama a matsayin ‘yan gudun hijira.

KU KARANTA:Tsaron kasa da kasa: Sufeto janar na ‘yan sanda zai karbi bakuncin kasa 194 domin taron INTERPOL

Wasu daga cikinsu na zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijra dake wasu jihohin Najeriya yayin da sauran suka tsallaka zuwa kasahen dake makwabtaka da Najeriya.

A yammacin Alhamis ne da misalin karfe 5:00 jirgin saman NAF mai lamba C130 ya dira a filin sauka da tashin jiragen sama na Yola dauke da ‘yan gudun hijirar.

Jami’an hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta shaida mana cewa ‘yan gudun hijirar da kansu suka nema a maidosu gida.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, daraktan hukumar kula da ‘yan gudun hijira, Lawal Hamidu ya ce, “ Babu wanda aka tilasta a cikin wannan aikin, ‘yan gudun hijirar ne da kansu suka nemi a maida su gida.”

Wasu daga cikin mutanen da suka dawon sun bayyana zamansu a Kamaru a matsayin wani zama maras dadi mai cike da halin damuwa.

Rikicin kungiyar Boko Haram wanda ya soma tun shekarar 2009 yayi sanadiyar rasuwar dubban mutane. Jihohi uku da yakin Boko Haram din yafi shafa sune Borno, Adamawa da Yobe wadanda ke Arewa maso gabas ta Najeriya.

A wani labarin mai kama da wannan zaku ji cewa, Sufeto janar na 'yan sanda Mohammed Adamu zai karbi bakuncin kasashe 194 domin taron INTERPOL a babban birnin tarayya Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya DCP Frank Mba ne ya bada wannan sanarwar inda ya ce taron zai gudana ne daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Agusta, 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel