Zanga-zangar juyun juya hali: Kungiyoyin Arewa 9 sun tsame hannunsu, sun bayar da dalili

Zanga-zangar juyun juya hali: Kungiyoyin Arewa 9 sun tsame hannunsu, sun bayar da dalili

Kungiyoyi tara cikin 15 da suka kafa hadin gwiwa na sake yin zanga-zangar juyin juya hali ta Revolutionow wasu jihohin arewa a ranar 22 ga watan Augusta sun tsame hannunsu daga tafiyar.

Sakateren kungiyoyin, Tanko Mustapha ne ya bayyana hakan cikin wata jawabi da ya yi yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar a daren ranar Laraba a Kaduna inda ya ce; "Muna son sanar da cewa a yau wadannan kungiyoyi tara sun cimma matayar janyewa daga zanga-zangar da Joint Northern Action ta kira."

Mustapha ya ce sun janye daga zanga-zangar ne saboda wasu dalilai.

"Mun janye zanga-zangar da muka shirin yi ne bayan munyi nazarin niyyar yin zanga-zangar da kuma irin matsalolin da za ta iya haifarwa musamman a Arewa da demokradiyar Najeriya.

DUBA WANNAN: Sunaye da mukami: Buhari ya yi wasu sabbin muhimman nade-nade 8 a ofishin Osinbajo

"Mun kuma gano cewar akwai wasu manufofi na boye da yasa aka shirya zanga-zangar baya ga yunkurin tilastawa gwamnati ta inganta rayuwar al'umma. Muna kuma ganin ba dole bane ayi zanga-zangar cikin lumana.

"Mun kuma yi nazarin irin abubuwan da zanga-zanga irin wannan ta haifar a kasashe kamar Libya da Yemen. Daga karshe mun yanke shawarar cewa yin zanga-zangar na ba za ta haifarwa kowa da mai ido ba.

"Duk da cewa gwamnati tana gazawa a wasu bangarori kamar tsaro da tattalin arziki, muna son mu dauki matsaya irin ta sauran kungiyoyin arewa na cewa za a iya shawa kan matsalolin ta hanyar tattaunawa a teburin sulhu ba sai an tayar da hankula ba.

"Saboda haka, daga yau, mun tsame hannun mu daga wannan tafiyar kuma muna kira ga al'ummar arewa suyi watsi da kiraye-kirayen yin zanga-zangan," inji Mustapha.

Mustapha ya kuma yi kira ga gwamnati ta gaggauta magance matsalolin da al'umma suke fama da su domin kiyaye afkuwar tashin hankali a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel