Oyo-Ita: Buhari da kansa ne ya nemi na koma bakin aiki

Oyo-Ita: Buhari da kansa ne ya nemi na koma bakin aiki

Shugbar ma’aikatan tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita ta bayyana dalilinta na dawowa bakin aiki bayan amsa tambayoyi daga hukumar yaki da cin hanci a rashawa (EFCC) akan zargin zambar naira biliyan 3.

Wata majiya a ofishinta ta bayyana cewa Oyo-Ita ta sanar da ma’aikaci na kusa da ita cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ta dawo ofishin domin ci gaba da aiki.

Don haka, ta bayyana cewa ya zama dole ta dawo sannan ta ci gaba da aikinta. Da farko dai ana ta rade-radin cewa Oyo-Ita ta yi murabus bayan matsin lamba da ta fuskanta daga EFCC da fadar Shugaban kasa.

Rashin ganinta a taron shirin rantsar da sabbin ministoci na kwanaki biyu ya dada rura wutar rade-radin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa abubuwa sun daidaita a ofishin shugabar ma’aikatan na tarayya.

KU KARANTA KUMA: Abin da yasa Buhari ya nada ni ministar harkokin mata - Sabuwar minitsa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa fadar Shugaban kasa ta bukaci shugabar ma’aikatan tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita da ta tsayar da shirinta na yin ritaya cikin gaggawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito daga wasu majiyoyi a jiya Laraba, 21 ga watan Agusta.

“An bukaci da ta ci gaba da jan ragamar ofishinta har zuwa lokacin da za a kammala bincike akan lamarin,” inji daya daga cikin majiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel