Daga karshe, an gano dalilin da yasa Buhari bai sake bawa Dambazau minista ba daga Kano

Daga karshe, an gano dalilin da yasa Buhari bai sake bawa Dambazau minista ba daga Kano

Bayanai sun fara bayyana a kan dalilin da yasa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai sake nada tsohon ministan harkokin cikin gida, Laftanal Janar Abdulrahmana Dambazau (mai ritaya) a matsayin minista ba a zangonsa na biyu.

Dambazau na daga cikin tsofin ministoci 18 da shugaba Buhari ya cire sunayensu daga cikin jerin sunayen mutane 43 da ya sake nada wa ministoci a zangonsa na biyu.

Jaridar 'The Whistler' ta rawaito cewa shugaba Buhari ya ajiye Dambazau ne bayan wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa ya same shi da laifin 'cin mutuncin aiki'.

Jaridar ta ce majiyarta ta bayyana mata cewa, Dambazau; tsohon shugaban rundunar sojojin Najerriya (COAS) daga 2008 zuwa 2010, ya gaza samun damar koma wa kujerarsa ne bayan an gano cewa yana da hannu wajen badakalar mayar da tsohon shugaban hukumar fansho da ya gudu, Abdulrasheed Maina, bakin aiki.

The Whistler ta ce dama shugaba Buhari ne da kansa ya zabi Dambazau domin bashi mukamin minista a karo na farko, a shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Kuruciya: Wani yaro mai shekaru 13 ya rataye kansa bayan budurwar da yake so a boye ta yi saurayi

Wata majiya, da ta nemi a boye sunanta, ta bayyana cewa Dambazau bashi da goyon bayan shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC a jihar Kano, mahaifarsa, a lokacin da shugaba Buhari ya zabe shi domin nada shi minista a 2015.

Tun kafin shugaba Buhari ya ajiye Dambazau, jaridar ta ambaci sunansa a cikin jerin sunayen ministoci 11 da basu cancanta su sake samun mukamin minista ba.

Hasashen jaridar ya bayyana cewa Dambazau ya gaza yin amfani da gogewarsa ta aiki wajen kawo karshen kalubalen tsaro, musamman a yankin arewa maso gabas da arewa ta tsakiya, da suka yi tsamari a zangon mulkin Buhari na farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel