Asiya da Atika, kwararrun masu garkuwa da mutane sun shiga hannu a jihar Kebbi

Asiya da Atika, kwararrun masu garkuwa da mutane sun shiga hannu a jihar Kebbi

Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kebbi sun yi nasarar cafke wata mata da ta kware wajen shirya garkuwa da mutane tare da karbar kudin fansa.

An kana Asiya tare da wata kawarta da suke aiki tare mai suna Atika Atiku a karamar hukumar Jega. Sauran 'yan kungiyar da ke aiki tare da Asiya da Atika sun gudu.

Asirinsu ya tonu ne bayan sun hada baki tare da yin garkuwa da wata yarinya mai shekaru uku.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kebbi, Garba Muhammad Danjuma, ya bayyana cewar jami'an 'yan sanda na atisayen 'Puff Adder' ne suka kubutar da yarinyar da suka yi garkuwa da ita.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban jam'iyyar APC da wasu mutane hudu

Kazalika, kwamishinan ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kama wani mutum, Sidi Danbuzu, wanda ya hada baki da wani mai suna Ahmadu Gardi tare da yin garkuwa da wani mutum, Alhaji Amadu, mazaunin kauyen Fadama a karamar hukumar Kangiwa.

Ya ce wadanda ake zargin sun karbi N600,000 daga hannun mutumin da suka yi garkuwa da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel