Jam’iyyar Shehu Sani ta yi watsi da hukuncin kotu akan zaben sanatan Kaduna

Jam’iyyar Shehu Sani ta yi watsi da hukuncin kotu akan zaben sanatan Kaduna

Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) a ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta, ta yi watsi da hukuncin kotun zabe da ke korar karar da ta shigar a gabanta game da zaben majalisar dokokin tarayya na 2019. Ta sha alwashin daukaka kara.

Da take Allah wadai da hukuncin kotun zabe akan karar da tsohon dan majalisa, Shehu Sani, wanda yayi takarar kujerar sanata na Kaduna ta tsakiya a karkashin PRP ya shigar, jam’iyyar tace hukuncin kotun ba komai bane face zamba daga bangaren shari’a.

Da take wofantar da hukuncin kotun, jam’iyyar PRP tace kotun zaben ta gaza ba ta damar da ta nema na sake kirga kuri’un.

A wani jawabi dauke da sa hannun Shugaban PRP a jihar Kaduna, Abdulrahman Danbirni, yace wanda ake karar, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress bai taba gabatar da shaida ko guda ba a gaban kotun domin tabbatar da nasararsa.

Danirni ya kuma yi zargin cewa lauyan da ya wakilc hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) akan lamarin ya kasance babban alkalin gwamnan jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Ba sanya: Yan sandan Jamus sun gano 4 daga cikin wadanda suka kai wa Ekweremadu hari

A cewar Danbirni, kotun zaben har ila yau ta gaza sanar da lauyan Shehu Sai ranar zartar da hukunci.

Yace hukuncin babu adalci sannan kuma yana nuni ga fashin zabe karara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel