Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da dan majalisa a Sokoto

Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da dan majalisa a Sokoto

Jami'an yan sanda a jihar Sokoto sun bazama neman wadanda sukayi garkuwa da dan majalisa mai wakiltan mazabar Denge/Shuni a majalisar dokokin jihar Sokoto, Aminu Magaji Bodai.

Wani dan'uwan dan majalisan ya bayyana cewa an yi awon gaba da shi ne misalin karfe 1:15 na daren Alhamis tsakanin Dange da Bodai.

Yace: "Ina mai tabbatar muku da cewa an yi garkuwa da dan'uwana. Har yanzu bamu san inda yake ba kuma wadanda suka saceshi basu tuntubemu ba."

Kakakin hukumar yan sanda jihar Sokoto, ASP Muhammad Sadiq Abubakar, ya tabbatar da wannan labari inda yace:

"Misalin karfe 1:30 na daren yau, mun samu labari a ofishin Denge cewa wasu yan bindigan kimanin 10, da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun shiga kauyen Bodai na karamar hukumar Denge Shuni kuma sukayi garkuwa da dan majalisa mai wakiltar Denge Shuni, Hanarabul Aminu Magaji Bodai."

Ya kara da cewa DPO ya kira kwamishanan yan sandan jihar wanda ya tura karin jami'ai inda abin ya faru.

KU KARANTA: Yankin Buhari, Arewa maso yamma ta samu manyan ministoci 10, fiye da kudu gaba dayanta - Ohaneaze, Afenifere sun yi ca

A bangare guda, gwamnatin jihar Zamfara suna farin cikin kwanaki 59 ba tare wani labarin kai hari ko garkuwa da mutane a jihar tun bayan sulhun da akayi da yan bindigan jihar.

Wannan na nuni da cewa matakin da sabon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kirkiro da zaman sulhu da masu bindiga yana haifan da mai ido

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel