Yanzu Yanzu: Oyo-Ita ta dawo bakin aiki bayan Buhari ya ki amincewa da murabus dinta

Yanzu Yanzu: Oyo-Ita ta dawo bakin aiki bayan Buhari ya ki amincewa da murabus dinta

Winifred Oyo-Ita, shugabar ma’aikatan tarayya, ta dawo bakin aiki a ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta biyo bayan kin amincewa da bukatarta na yin ritaya da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

A makon da ya gabata ne Oyo-Ita ta aika wasikarta ga Shugaban kasar kai tsaye biyo bayan matsin lambar da ta fuskanta daga yaranta kan ta ajiye aikin.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta binciki Oyo-Ita kwanan nan kan zargin cewa tayi amfani da kamfanoni wajen samun kwangiloli a lokacin da take a matsayin sakatariyar din-din-din kafin nada ta a matsayin shugabar ma’aikata da Buhari yayi a 2015.

Shugabar ma’aikatar ta karyata batun kasancewa cikin kowani zamba.

Tun bayan da EFCC suka gayyace ta Oyo-Ita ta kaurace ma aikinta, amma a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta sai ta halarci taron rantsar da ministoci bayan ganawar da tayi da Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Abba Kyari.

Sai dai ga dukkan alamu shugaba Buhari bai gamsu da rade-radin da ake akanta ba inda ya ki amincewa da ritayarta daga aiki.

KU KARANTA KUMA: Allah mai yadda ya so: Kalli ministan Buhari wanda ya fara daga matsayin Masinja a rayuwa

An tattaro cewa duk wani kira-kirayen wayan Oyo-Ita bai shiga ba, amma daya daga cikin hadimanta yace ta ajiye kamarin a gefe sannan za ta yi Magana a lokacin da ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel