Kotu ta ba hukumar AMCON damar karbe kadarorin Donald Duke

Kotu ta ba hukumar AMCON damar karbe kadarorin Donald Duke

Babban kotun tarayya da ke Legas ta bada izni ga hukumar AMCON mai kula da kadarorin Najeriya ta karbe wata kadara da tsohon gwamnan Kuros Riba, Donald Duke ya mallaka.

Alkali mai shari’a Chuka Obiozor shi ne ya bada dama ga hukumar kasar ta dawo da wasu kadarori da Donald Duke ya mallaka a cikin Garin Ikoyi da ke Legas hannunta saboda tarin bashi.

A na bin tsohon gwamnan da Mai dakinsa Misis Owanari Bob-Manuel Duke tsohon bashin kudi har N537, 334, 360.77 da sunan wani kamfaninsu watau Stonehedge Investment Limited.

Wannan ya sa hukumar AMCON ta dumfari kotu a cikin farkon Watan Agustan nan ta na neman a dawo da kadarorin Duke karkashin kulawarta. Kotu ta amince da wannan a makon nan.

KU KARANTA: Haraji: Obasanjo, Davido, da Sanata Omisore su na cikin masu laifi a Najeriya

AMCON ta fadawa kotu cewa Donald Duke ya bada gidansa mai lamba na 3 da ke kan titin Temple Road, a Garin Ikoyi da sunan jingina a lokacin da zai karbi bashin da yanzu ya gaza biya.

Hukumar kasar ta AMCON ta kuma roki kotu ta daskarar da kudin da ke cikin asusun bankin Donald Duke da Maidakinsa da kamfaninsu, har sai zuwa lokacin da a ka karkare bincike.

Wannan kudi da su ka haura Naira miliyan 500 sun taru ne a dalilin ruwan da ke cikin bashin da ‘dan siyasar ya karba a baya. Yanzu dai bashin ya yi Duke da wanda a ke kara katutu a kai.

Kotu ta ba AMCON damar da ta nema, bugu da kari an haramtawa wanda a ke tuhuma damar tura kudi ko ta wani irin hanya a cikin akawun din su na banki inda a ka dage kara zuwa Satumba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel