'Yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban jam'iyyar APC da wasu mutane hudu

'Yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban jam'iyyar APC da wasu mutane hudu

Wasu 'yan bindiga sun harbe mataimakin shugaban jam'iyyar APC na mazaba ta 5 da ke yankin karamar hukumar Oyigbo a jihar Ribas.

Mataimakin shugaban jam'iyyar, Edward Okechukwu, da ne wurin Azuogu, babban basaraken masarautar Ndoki, kuma yana daga cikin sauran mutane hudu da 'yan bindigar suka hallaka da sanyin safiyar ranar Litinin.

Mazauna yankin sun yi zargin cewa 'yan indigar sun fito ne daga yankin Ilori na garin Ogoni a karamar hukumar Tai da ke jihar ta Ribas.

DUBA WANNAN: Bashin miliyan N537.3: Kotu ta sahale wa AMCON ta kwace katafaren gidan tsohon gwamnan PDP

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar, dauke da muggan makamai da suka hada da bindiga samfurin AK47, sun kara raunata wasu mutanen a wasu kauyuka guda biyu.

Kazalika, sun lalata kayayyakin jama'a tare da yin awon gaba da kayan kudi masu yawa daga kauyukan da suka kai harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel