Farawa da iyawa, wasu sabbin ministoci sun shiga ofis a ranar rantsuwar kama aiki

Farawa da iyawa, wasu sabbin ministoci sun shiga ofis a ranar rantsuwar kama aiki

-Ministan ilimi da na lafiya sun shiga ofis a ranar da suka yi rantsuwar kama aiki

-Adamu Adamu ya sake komawa bisa kujerarsa ta ministan ilimi yayin da ma'aikatar lafiya tayi sabon minista wato Osagie Ehanire

Sabbin ministocin lafiya da ilimi wadanda Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar ranar Laraba sun shiga ofis a ranar da aka rantsar da su domin kama aiki.

Wadannnan ministocin sun hada Osagie Ehanire wanda shi ne babban ministan lafiya da Olurunimbe Mamora a matsayin karamin ministan lafiya. Sai Adamu Adamu da Emeka Nwajuibu a matsayin babban da karamin ministan ilimi.

KU KARANTA:Sabbin ministocin Buhari taron tsintsiyane babu shara, inji PDP

Rahotanni daga jaridar Premium Times sun bayyana mana cewa Ehanire da Mamora sun dira ma’aikatar lafiya dake Abuja ‘yan sa’o’i kadan bayan sun kammala rantsuwar karbar aiki daga wurin Shugaba Buhari.

Da yake zantawa da ‘yan jarida Ehanire ya ce zai yi aiki a bisa umarnin Shugaban kasa na tabbatar da an samar da kayayyakin kula da lafiya musamman ga al’ummar talakawa.

Har ila yau, ministan ya ce a shirye yake domin ya taimkawa shugaban kasa wurin cinma daya daga cikin manufofinsa tun a lokacin kamfe, na samar da kayayyakin kiwon lafiya su wadata cikin al’umma.

A bangare guda kuwa Adamu Adamu da Nwajiuba ne suka isa ma’aikatar ilimi da misalin karfe 2:45 na ranar Laraba. Rahotanni sun tabbatar mana cewa daga fadar Shugaban kasa wurin rantsuwar kama aiki suka fito.

Adamu Adamu wanda shi ne babba a ma’aikatar ya yi jawabi ga ilahirin ma’aikatansa inda ya zaburar da su a kan cewa aikin da suka saba yi ba wai bari za ayi ba a don haka kowa ya kara zage dantsensa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel