Daga karshe: Wadume ya bayyana yadda ya zama hamshakin mai arziki

Daga karshe: Wadume ya bayyana yadda ya zama hamshakin mai arziki

- Alhaji Hamisu Bala wanda akafi sani da Wadume ya shaidawa 'yan sanda cewa ya samu arzikinsa ne ta sana'ar sayar da kifi

- Wadume ya kuma ce ya kan damfari mutane yana sayar musu da magungunan gargajiya na bogi ya amshe musu miliyoyin kudi

- Amma ya musanta cewa yana aikata garkuwa da mutane don karbar kudin fansa kamar yadda 'yan sanda ke zarginsa

Alhaji Hamisu Wadume wani mutum na jihar Taraba da 'yan sanda suke zargi da aikata garkuwa da mutane ya musanta cewa shi mai garkuwa da mutane ne inda ya ce 'Yan sanda sunyi kuskure kan alakantanshi da laifin.

Wadume ya shaidawa shugabanin 'Yan sanda a hedkwatan rundunar da ke Abuja a ranar Talata cewa ya samu arzikinsa ne ta sana'ar kamun kifi da ya kwashe shekaru masu yawa yana yi a cewar majiyoyi da dama da suka hallarci zaman amsa tambayoyin.

"Amma ya amsa cewa yana damfara wato 419 inda ya ke sayar wa masu magungunan gargajiya na bogi yana samun miliyoyin kudade," kamar yadda majiyar 'yan sanda ta shaidawa Premium Times.

"Ya doge cewar baya garkuwa da mutane don kudin fansa kuma ba ta hanyar 419 ya tara dukkan arzikinsa ba."

DUBA WANNAN: Fitar da bidiyon Wadume da 'yan sanda su kayi yana ci mana tuwo a kwarya - Kwamitin bincike

An sake kama Wadume ne a daren ranar Litinin a garin Kano kuma aka garzaya da shi zuwa Hedkwatan 'Yan sanda da ke Abuja a ranar Talata wadda hakan ya kawo karshen farautarsa da akeyi.

A baya, wasu sojojin Najeriya sun kashe wasu 'yan sanda 3 da farar hula a jihar Taraba yayin da suka budewa motar da ke dauke da shi wuta kuma suka tafi da shi hedkwatansu suka cire ankwan da ke hannunsa kamar yadda ya fadi a wani faifan bidiyo.

Bayan hakan ne ya tsere ya rika buya har zuwa lokacin da asirinsa ya sake tonuwa aka kamo shi a Kano.

Kisan 'yan sandan da farar hular ya janyo sa-in-sa tsakanin rundunar 'yan sanda da ta soji inda daga baya aka kafa kwamitin bincike da ya kunshi sojoji, yan sanda da wasu hukumomin tsaro don sanin gaskiyan abinda ya yi sanadin kisan 'yan sandan uku a Taraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel